1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rashin adalci na daga cikin musabbabin rikicin Najeriya

August 13, 2014

Babban taron neman zaman lafiya da habaka tattalin arzikin arewa maso gabashin Najeriya ya yi kira da hada kai da gudanar da kyakkyawan shugabanci don magance matsalar rashin tsaron.

Symbolbild Gewalt in Nigeria
Hoto: SEYLLOU DIALLO/AFP/Getty Images

An kammala taron masu ruwa da tsaki kan kokarin da ake yi na samar da zaman lafiya da bunkasar tattalin arzikin kasa na yankin arewa maso gabashin Najeriya wanda ke cikin mummunan yanayi wanda asusun raya kasa na Majalisar Dinkin Duniya ya shira a garin Gombe.

Taron ya samu halartar dukkanin masu ruwa da tsaki a fannin wanzar da zaman lafiya da suka hada da gwamnatocin jihohin yankin arewa maso gabashin Najeriya da jami'an tsaro da masana tattalin arzikin kasa gami da malaman jami'a da sarakuna da kuma shugabannin addini.

Babban abinda wanda taro ya fi maida hankali shi ne fahimtar abinda ya haifar da wannan rikici da ya gurgunta shiyyar arewa maso gabashin Najeriya tare da samun shawarwari daga masana domin magance matsalar.

Rashin kyakkyawan shugabanci ya taka rawa

Kwararru da suka gabatar da kasidu a wannan taron sun yi imanin cewa rashin adalci da kuma rashin shugabanci na gari shi ne kashin bayan wannan rikici inda kuma suka kauda tunanin da wasu ke yi na danganta masu tada kayar bayar da wani addini ko kuma wasu kungiyoyi da ke kasashen ketare.

"Gwamnati na iya kokarin magance rikicin kasar..."-Shugaba JonathanHoto: DW/U. Musa

Sun kuma nemi shugabanni su nemo hanyoyi na binciken harkokin matasa da kuma magance zaman kashe wando da miliyoyin matasan Najeriya ke yi, wanda suka ce yana taka muhimmiyar rawa wajen shigar matasa cikin kungiyoyin masu tada kayar baya.

Yayinda aka karfafa zargin gwamnatin Najeriya na yin sakaci kan magance matsalar, gwamnatin na ganin sam ba haka lamarin ya ke ba don kuwa jami'an tsaron kasar wanda gwamnatin Najeriya ta tura suna iya kokarinsu kamar yadda Abba Moro ministan kula da harkokin cikin gida ya bayyana.

"Rundunar sojojin Najeriya suna kokari fiye da yadda suka yi a baya kuma a shirye suke su kawo karshen wannan yaki cikin kankanin lokaci. Duk wanda ya ke zargin gwamnatin Najeriya cewa bata komai, to son zuciya ne. Saboda haka ina mai tabbatar muku cewa gwamnatin tarayya za ta yi amfani da dukkanin abinda ta ke da shi na ganin an kawo karshen wannan matsalar."

Ba nan gizo ke saka ba

Sai dai da dama da suka halarci wannan taro ba su yarda da matsayin gwamnatin ba musamman ganin yadda ake ci gaba da samun hare-hare da ma yadda 'yan kungiyar ke ci gaba da kwace wasu muhimman garuruwa a yankin arewa maso gabashin Najeriya bayan da suka kori jami'an tsaron da ke wuraren.

Ga Sarkin Musulmi na Najeriya Alhaji Sa'ad Abubakar wanda sarkin Bauchi Alhaji Rilwan Sulaiman Adamu ya wakilta ya bayyana cewa "jama'a su ci gaba da hakuri tare da yin addu'a don samu sauki wannan matsalar."

Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad AbubakarHoto: Sultan's Office

Kungiyoyin mata da kuma na shugabannin arewacin Najeriya sun bukaci gwamnonin wannan yanki su hada kai domin ganin an samo bakin zaren warware wannan rikici wanda aka yi imanin cewa yana da sarkakiya kuma ya zama dole a yi dukkan abu mai yiwuwa na ganin an kashe wutar wannan rikicin nan ba da dadewa ba.

Mawallafi: Al-Amin Suleiman Mohammed
Edita: Mohammad Nasiru Awal

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani