Ana ci gaba da fargaba kan halin da Boris Johnson ke ciki
April 7, 2020Talla
Tuni fadar gwamnatin kasar ta sanar da sarauniyar Ingila halin da Boris Johnson ya ke ciki, kana kuma ta bayyana matakin nada Dominic Raab ministan harkokin wajen kasar, a matsayin wanda zai wakilci firaministan a duk inda bukatar kasancewarsa ta taso.
A ranar Lahadin da ta gabata ne dai rahotanni suka ce firaminista Boris Jonhson ya nufi asibiti don kara kula da lafiyarsa, lamarin da ya kara tsananta a yammacin jiya. Shugaban Amirka Donald Trump da na Faransa Emmanuel Macron da firaminsitan kasar Italiya Giuseppe Conte, duk sun nuna damuwa kan tsanantar rashin lafiyar ta Boris Johnson, tare da yi masa fatan samun sauki.