Rashin tabbas ga taron zaman lafiyar Siriya
May 22, 2013Canje canjen da ake samu a yakin da ake yi a kasar ta Siriya tsakanin dakarun gwamnatin shugaba Bashar Al-Assad da sojojin 'yan tawaye ya sa ana nuna shakku game da sabon taron.
Hakan dai na zuwa ne yayin da a wannan Laraba ministocin harkokin wajen kasashe 11 sun hallara a Amman babban birnin kasar Jordan don neman mafita daga rikicin Siriya. Babban batu a jadawalin wannan haduwa shi ne babban taron zaman lafiya da ake shirin gudanarwa a birnin Geneva, wanda sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov suka amince a kai yayin wani taro a makon jiya. Sai dai ana nuna shakku ko taron zai yiwu. Da farko a kwanakin bayan nan an jiyo shugaban Siriya Bashar al-Assad na cewa ko da yake yana maraa da taron kuma yana goyon bayansa amma ya nuna shakkunsa.
Daga bangaren 'yan adawar Siriya ma, dole ne ministocin harkokin wajen dake taro a Jordan su yi kokarin shawo kansu, domin hadaddiyar kungiyar 'yan adawar Siriya ta gindaya sharudda game da babban taron, kamar yadda kakakin 'yan adawar Hisham Marwah ya nuna a wata hira da DW.
"A sashe na biyar na kundin tsarin mulkin kawancen 'yan adawa na kasa na watan Nuwamban 2012, mun nuna a fili cewa duk wata tattaunawa da wannan gwamnati ba za ta yiwu ba. Duk wata kwaskwarima da za mu yi wa wannan sashe dole sai an zartas da wani kuduri tukuna."
Sauyin alkibla a yakin Siriya
Sai dai Marwah ya kara da cewa a cikin kwanaki masu zuwa za su tattauna game da matakan da za su dauka.
Ba ya ga kokarin shawo kan marikitan na Siriya da su halarci babban taron zaman lafiya, wani batun da ministocin harkokin wajen da suka hallara a birnin Amman za su duba shi ne lokacin gudanar da tarron.
Wani rahoto da mujallar Der Spiegel ta nan Jamus ta buga ta rawaito hukumar leken asirin Jamus na bayani ga sabuwar alkiblar da rikicin sojin Siriya ya dosa. Ta ce yanzu sojojin Assad sun yi karfi fiye da lokutan baya, inda ma suka fatattaki 'yan tawaye daga wasu yankunan babban birnin kasar Damaskus kana sun katse wasu hanyoyin samun kayaki ga 'yan tawaye daga kudancin kasar.
Muddin wannan labarin ya tabbata gaskiya to gwamnatin Assad ba za ta nuna wata sha'awar taron sasantawa da 'yan tawayen nan kusa ba, inji Hisham Marwah kakakin 'yan adawa.
"Za a ci-gaba da wannan yaki har sai gwamnati ta samu wata kyakkyawar madogara ta shiga taron samar da zaman lafiyar."
A guji sanya dogon buri ga taron
A dangane da jajircewar da marikitan na Siriya ke yi na ci-gaba da yaki, Joachim Hörster memba na kwamitin harkokin wajen majalisar dokokin Jamus, ya jawo hankali da a guji sanya dogon buri ga taron neman mafita daga rikicin na Siriya.
"Gagarumin ci-gaba ne na duba yiwuwar shirya wannan taron bisa la'akari da halayyar masu rikicin a Siriya. Domin kawo yanzu duk wani mataki da aka dauka ta wannan fuskar sai an hada da gindaya sharudda. 'Yan adawa na bukatar sai Assad ya sauka kafin a yi taro, ita kuma gwamnati ta ce ba za ta zauna kan teburin shawarwari da 'yan ta'adda ba."
Har in dai an kai ga shirya wannan taro to muhimmin abu shi ne bai kamata a hada rikicin Siriya da wasu muhimman batutuwan na yankin mai daure kai ba, wato kamar shirin nukiliyar kasar Iran.
Mawallafa: Kersten Knipp / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Saleh Umar Saleh