1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rashin tabbas game da tsagaita wuta a gabashin Ukraine

September 3, 2014

Yayin da shugaban Ukraine ke fatan cimma zaman lafiya a gabashin kasar, takwaransa na Rasha ya gabatar da wani shiri ne da nufin kawo karshen rikici a yankin.

Gipfeltreffen in Minsk Putin und Poroschenko 26.08.2014
Hoto: Reuters/Sergei Bondarenko/Kazakh Presidential Office

Shugaban Ukraine Petro Poroshenko ya ce yana fata wani shirin zaman lafiya ga yankin gabashin kasar mai fama da rikici, zai fara aiki a ranar Jumma'a, yana mai cewa al'ummar Ukraine na goyon bayan zaman lafiya dari bsa dari, amma shugabannin siyasa na son nuna karfi a filin daga. Kalaman na Poroshenko sun zo ne yayin da a nasa bangaren shugaban Rasha Vladimir Putin ya gabatar da wani shiri da nufin warware rikicin na Ukraine.

Petro Poroshenko ya yi wadannan kalaman gabanin taron wakilan kasashen Ukraine, Rasha da kuma na kungiyar tsaro da hadin kai a Turai da aka shirya gudanarwa a Minsk babban birnin kasar Belarussia a ranar Jumma'a da nufin kawo karshen rikicin tsawon watanni shida tsakanin dakarun gwamnatin birnin Kiev da 'yan tawaye magoya bayan Rasha da ke gabashin Ukraine.

Tattauna batun tsagaita wuta a gabashin Ukraine

Ba za mu yarda da yaudara daga Putin ba - Arseny YatsenyukHoto: Reuters

Da ma tun farko ofishin shugaban kasar ta Ukraine ya ce shugaba Petro Poroshenko da takwaransa na Rasha Vladimir Putin suna dab da cimma yarjejeniya a kan tsagaita wuta a gabashin kasar. Sai dai sanarwar ta shige wa mutane duhu kuma ba bu wata alamar da ke nuni da cewa za a daina fadan. Kakakin majalisar tsaron kasar Ukraine Kanal Andrei Lysenko ya tabbatar da tattaunawar tsakanin shugabannin biyu.

"Sakamakon tattaunawar shi ne tsagaita wuta a yankin Donbas. An amince da wasu karin matakai na yadda za a taimaka a samar da zaman lafiya."

Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban Rasha Vladimir Putin ya fada yayin wata ziyara kasar Mongoliya cewa ya gabatar da wani shiri mai rukunai bakwai da ke da nufin kawo karshen yakin da ake tsakanin sojojin Ukraine da na 'yan aware masu ra'ayin Rasha tare kuma da yin musayar firsinoni tsakaninsu.

Take-taken kaurace wa sabbin takunkumai

To sai dai Firaministan Ukraine Arseny Yatsenyuk ya yi watsi da shawarar ta Putin ta samar da zaman lafiya a Ukraine yana cewa wani yunkuri ne na yaudarar kasashe yamma a jajiberen taron kolin kungiyar NATO.

"Ukraine na bukatar sabon kudurin tsaron kasa da zai zayyana shin wane ne mai ta da zaune tsaye wane ne kuma ke cikin hatsari. A cikin sabon kudurin dole a dauki Rasha a matsayin kasa mai ta da fitina wadda kuma ke zama baraza ga tsaron kasarmu."

Yayin da taron wakilan Ukraine da Rasha a Minsk zai duba batun wanzar da zaman lafiya a gabashin Ukraine, su kuwa shugabannin NATO da za su yi taron kolin kwanaki biyu a Birtaniyya a ranakun Alhamis da Jumma'a za su duba batun kara yawan dakarunsu a kan iyakokin kungiyar na gabashin Turai.

Zanen alamar yakin cacar baka a rikicin Nato da RashaHoto: picture alliance/AP Photo/Mindaugas Kulbis

Tuni dai shugaban Amirka Barack Obama ya sanar da tura karin sojojin saman Amirka da kuma jiragen saman yaki yankin Baltik.

"Mun tura karin jiragen sama ga tawagar sanya ido a sararin samaniyar yankin Baltik. Wannan aiki ne da wasu karin kasashe 14 na NATO suka ba da gudunmawa a cikin shekaru 10 da suka wuce, kuma yanzu muna ci gaba da tura karin sojoji da jiragen sama a kasashen yankin Baltik."

Sai dai gabanin taron kolin na NATO, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel na kokarin kawar da fargabar munin rikici tsakanin kungiyar kawancen da kuma Rasha. Ta ce ba ta jin Rasha za ta dauki matakin kai farmaki a yankin na Baltik.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman