Rashin tabbas kan warware rikicin Iran
April 20, 2026
Yayin da ya rage kwanaki kalilan yarjejeniyar tsagaita wutar yakin Iran da Amukra ta makonni biyu ta kare, alamu na nuni da cewa sake cimma sabuwar masalahar tsawaita tsagaita wutar na cikin halin rashin tabbas.
Babban batun da ke janyo takaddamar gaza cimma matsaya a kan wannan rikici shi ne makomar mashigin Hormuz da Iran ta datse, wanda ya ke da matukar tasiri ga tattalin arzikin duniya, sakamakon jigilar mai da gas da sauran kayayyakin da ake gudanarwa a wannan gabar ruwa, daga bisani Iran ta aminta da budewa, amma jim kadan ta sake toshe hanyar, domin nuna fushi kan yadda sojin Amurka suka kwace mata jirgin dakon mai ranar Lahadi, lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa tashar ruwan Bandar Abbas, bayan shafe tsawon sa'o'i shida suna ja-in-ja, inda Amurka ta lalata injin jirgin bayan harbinsa.
Dalilin ke nan da ya sanya ma'aikatar harkokin wajen Iran ta bakin kakakinta Esmaeil Baghaei ke cewa hakika Washington ba da gaske take ba, wajen bin hanyoyin diflomasiyya domin kawo karshen wannan rikici, a don haka babu ta yadda za a yi Tehran ta sauya daga matsayarta ta asali game da muradan da ta sanya a gaba.
Pakistan ce kasar da ta taka muhimmiyar rawa wajen kokarin daidaita al'amura ta hanyar jagorantar zaman farko a birnin Islamabad, wanda yanzu haka ake kokarin shiga zagaye na biyu idan komai ya tafi yadda aka tsara.
To sai dai kwararriya a sha'anin diflomasiyya Maleeha Lodi, wadda ta taba zama jakadiyar Pakistan a Amurka da Burtaniya da kuma Majalisar Dinkin Duniya, ta ce har yanzu suna da kwarin gwiwar shawo kan rikicin ta hanyar laluma.
''Za mu ci gaba bin hanyoyi na diflomasiyya don kawo karshen wannan yaki, kuma a zaman farko wasu da dama na hakilon cewa an rabu dutse hannun riga, to sam ba haka lamarin yake ba, tabbas ba komai aka samu daidaito a kai ba, amma dai da babu gwara ba dadi. Pakistan na ci gaba da tuntubar juna ta hanyar babban hafsan sojinta Field Marshal Asim Munir, wanda yake magana da shugaban Amurka Donald da kuma jagororin Iran a daya bangaren. Ina ganin yanzu zabi yana hannun Amuka na cimma masalaha''.
Game da cece-kucen da ake ta yi musamman a Amurka kan cewa Isra'ila ce ta jefa Amurka cikin wannan yaki, a wannan rana ta Litinin an jiyo shugaba Trump na musanta hakan, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na Truth Social, yana mai jaddada cewa babu ruwan firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu wajen ingiza shi far wa Iran da yaki, face harin da Hamaz ta kai wa Isra'ila ranar 7 ga Oktoban 2023, wanda ya farfado masa da burinsa na rayuwa da ya kudurce na dakile shirin Iran na mallakar makamin nukiliya.
To sai dai a lokacin masu shiga tsakani ke kokarin zuba wa wutar yakin ruwan sanyi don kashe ta, shi ko firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu cewa ya yi da sauran tsalle kan muradin da ya sanya a gaba.
''Mun kafa tutarmu a zirin Gaza har zuwa dutsen Hermon da ke Syria wanda ya raba ta da Lebanon, kuma yanzu haka mu ke da iko da sararin samaniyar yankin baki-daya, wanda ke nuna cewa mun samu galaba a kan yankunan da ke dasawa da Iran da ake kira da Iranian axis. To amma fa muna da sauran aikin da ba mu karasa ba, kuma duniya ta aminta da yadda muke kare kanmu, muke ba da kariya ta jin kai ga al'umma. Mu da babbar aminiyarmu Amurka mun dauki gabaren ba da kariya da ta dace''.
Iran ta sanar da cewa hare-haren Amurka da Isra'ila sun halaka mata mutane kimanin 3,375. Wadanda suka hada da mata 496 da kuma kananan yara 383. Kamar yadda babban jami'in binciken kiwon lafiya da shari'a na kasar Abbas Masjedi Arani ya tabbatar.
To sai dai alkaluman sun saba da na kungiyar kare hakkin 'dan adam ta kasar Norway mai suna Hengaw, wadda ta ce daga ranar 28 ga Fabarairu da aka fara yakin zuwa ranar 8 ga Afirilu da aka tsagaita wuta, kimanin mutane 7,650 suka rasa rayukansu a Iran.