Rufe makarantu sama da 1,500 a Mali
September 16, 2025
Modibo Sanogo guda ne daga cikin malaman makaranta da barazanar kungiyoyin jihadi ta dagulawa lissafi a Mali. Batun koyar wa batu ne mai alakaka da rayuwar malamin da a can baya ke koyarwa a wata makaranta da ke birnin Farako a tsakiyyar Mali inda a shakarun baya-bayan nan kungiyoyi da ke kokarin kafa daular Musulunci ke cin karensu babu babbaka.
Shi dai Modibo Sanogo ya rungumi aikin koyarwa ne gadan-gadan a shekarar 2018 bayan samun shahadar cancartar koyarwa ta CAP a makaranta horon malaman makaranta ta birnin Farako da ke a yankin Segou.
Tun a wannan lokaci ne Modibo da matarsa ita ma malamar makaranta da 'yan'yansu guda biyar ke zaune a wannan birni kafin lissafi su tsici Talatarsu a Laraba a 2019, abin da Modibo ya ce ba zai taba mantawa ba.
''Wasu mutane dauke da makamai fuskokin su a rufe sun sallamo a makarantarmu tare da yi wa malamai gargadi da kuma barazana. 'Yan jihadin sun yi gaskuwa da wasu malamai tare da kone kayan karatu sannan kuma suka umurcemu da mu fice daga makarantar saboda sun ce ba a bukatar ilimin boko na zamani.''
A ranar 13 ga watan Disamba na 2019, wasu mutane dauke da makamai da ake kyautata zaton masu ikirarin jihadi ne sun yi dirar mikiya a birnin Farako, inda suka yi garkuwa da kantoman birnin Ali Cisse a gaban idanuwan Modibo da takwarorinsa malaman makaranta. Wannan lamarin ya yi matukar tsoratar da Modibo da takwarorinsa.
''Ba mu taba ganin irin wadannan makamai ba. Dole ne wannan lamari ya yi matukar firgitar da mu.
Duba da girman wannan barazana ta kungiyoyin jihadi, ma'aikatar ilimi ta Farako ta yanke shawarar rufe makarantu sama da 100 a wannan yanki na Mali, lamarin da ya tilasta wa dubban dalibai zaman gida tare da jefa makomar iliminsu cikin hali na rashin tabbas.
''Abin takaici shi ne muna da adadin dalibai kusan 15,000 da muke korantarwar, amma daga cikin su ba a samu yara ko da 200 suka yi nasarar komawa wani yanki domin ci gaba da zuwa makaranta.''
Dalibai kusan 14,000 ne suka rasa damar zuwa makaranta a birnin na Farako, yayin da malamai sama da 400 suna ji suna gani suka bar aiki.