Rashin tsaro a Pakistan gabanin zabe
May 9, 2013A cikin wata wasika da jagoran kungiyar ta Taliban Hakimullah Meshud ya baiyana ya ce ya ba da izini ga 'ya'yan kungiyar domin kai hare-haren a ko-ina cikin kasar domin kawo tsaiko ga zabubukan na gama gari.
Yanzu haka dai wasu 'yan bindiga na yin garkuwa da dan tsohon firamininista Yusuf Raza Gilani wanda suka sace a wajan wani gangamin siyasa a lardin Benjab. Wasu rahotannin kuma na cewar 'yan bindigar sun kashe daraktan yakin neman zabe na Haider Gilani sannan shi kansa ya samu rauni a wani hari da suka kai. Gwamnatin Pakisatan dai ta kudiri aniyar jibge sojoji kusan dubu 90 a yankin arewa maso yammacin kasar domin tabbatar da tsaro a lokacin zabubukan wadanda ke cike da tarihi.
Mawallafi: Abdurrahmane Hassane
Edita: Mohammad Nasiru Awal