1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: INEC na fargabar rashin tsaro

January 10, 2023

Kasa da watanni biyu a gudanar da babban zabe na a cikin Tarayyar Najeriya, Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta kasar INEC, ta ce babban zaben da ke tafe na fuskantar barazanar tsaro da ka iya tilasta dage shi.

Najeriya | Zabe | INEC | Tsaro
Kalubalen rashin tsaro ga hukumar INEC a Najeriya yayin zaben da ke tafeHoto: Reuters/S. Maikatanga

Kama daga sashen arewacin kasar zuwa na kudancinsa dai, ana kallon ta'azzarar rashin tsaro a ko'ina cikin Najeriyar. An dai kame soja an kuma sake kai hari a jirgin kasa, ko bayan zubar jinin da ke ta karuwa kusan a ko'ina gabannin zaben. Abun kuma da ya tayar da hankalin Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta kasar INEC, inda ta ce karuwar rashin tsaron ka iya janyo dage zaben ko kila ma rushe shi. Koda yake har ya zuwa yanzu kakakin gwamnatin kasar Lai Mohammed na bayar da tabbacin iya zaben duk da jerin rigingimun da ke gudana a kasar, hukumar ta INEC ta ce karuwar barazanar na iya kawo cikas ga shirye-shiryenta da kila ma lafiya da kwanciyar hankali na dubban 'yan hidimar kasa da ke zaman jami'an  zaben. Mai magana da yawun hukumar ta INEC Zainab Aminu ta bayyana cewa, ana bukatar gyara kafin a samu biyan bukatar kowa yayin zaben. Tsoro kan rashin tsaro a cikin tsarin zaben Najeriyar dai, na iya shafar ingancinsa da kila ma karbuwa a ciki da ma wajen kasar. 

Ba ya ga rashin tsaron dai, akwai rashin karbar katuna ga masu kada kuri'a da damaHoto: DW

#b#An dai kai hari sau dai-dai har 50 a  cibiyoyin hukumar zaben, a wasu jihohin kasar 15. Ko a tsakanin masu takama da siyasa a kasar dai, amfani da fasaha ta zamani wajen yin zaben na janyo tsoron ba-zatan da sakamakon zaben ka iya yi. Tuni dai wasu jam'iyyun suka fara neman dakatar da na'urar BVAS wacce ke shirin tantance masu zaben, tare da aika sakamakonsa kai tsaye zuwa na'urar computer. Koda yake Najeriyar ta gudanar da zabuka cikin tsakiyar rashin tsaro a can baya dai a fadar Mohammed Lawal Nalado da ke zaman shugaban jam'iyyar Accord Party, akwai babban sauyi a yanayin rashin tsaron da fagen siyasar kasar ke fuskanta yanzu. Ko ma ya take shirin da ta kaya a tsakanin masu neman hana yin zabe da masu fatan dama, rashin tsaron dai na zaman hujja a banagren 'yan mulki na kasar can baya. Kuma ko a yanzu ma a fadar Faruk BB Faruk da ke sharhi kan siyasar kasar, masu mulkin Najeriyar na iya fakewa cikin rashin tsaron da niyyar cika buri. Kwanakin da ke tafe dai na da tasirin gaske, ga kokarin fidda dabaru domin samun nasara a bangaren masu siyasar da ke ta neman mulkin ko ta halin kaka.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani