Rauni a dokokin sayar da makaman Jamus
May 31, 2013To amma duk da haka, makaman kirar Jamus suna ci gaba da daukar hankali da shiga kanun labbarai a ko ina cikin duniya. Jamusawan sun fi nuna bacin ransu, idan manyan bindigogi da sauran makamai suka kasance ana amfani dasu a yankunan dake fama da yaki ko wasu rikice-rikice na siyasa, saboda burin dokokin kasar masu tsanani, shine a hana makaman na Jamus su watsu a yankuna dake fama da yaki ko a rika amfani dasu domin tauye hakki da yancin jama'a.
Tambayar farko ita ce: idan har gwamnatocin na Jamus suna kiyaye matakan bincike masu tsanani domin hana makaman kasar shiga yankunan yaki, yaya akan yi irin wadannan makamai suke isa can? A shekara ta 2011 da 2012 an kama makamai masu yawan 5100 ne da aka yi kokarin wucewa dasu ta iyakokin Jamus ta hanyoyi na haramun. Ofishin kididdiga dake birnin Cologne yayi kiyasin cewar kashi 10 cikin dari na makaman da aka yi kokarin sumogarsu zuwa ketare daga iyakokin na Jamus suna wucewa a zahiri, yayin da akan tare akalla kashi 90 cikin dari.
Ofishin yace a zarihi, fasa-kwarin makaman na Jamus zuwa ketare yakan samu ne a sakamakon rauni a matakan bada izinin sayar da makaman a ketare, inda ake da misalai inda makaman da Jamus ta bada izinin sayar dasu a ketare sukan kare a yankunan dake fama da yake-yaki, kamar yadda rundunan yan sandan Mexico take amfani da manyan bindigogi daga Jamus domin yaki da manyan masu aikata laifuka na wannan kasa. Wani misalin kuma shine yadda makaman na Jamus suka bullo a yakin basasan kasar Libya. Katja Keul, yar majalisar dokokin taraiya daga jam'iyar Greens tace wadannan misalai guda biyu sun nuna cewar akwai rauni mai yawa tattare da cinikin makaman na Jamus zuwa ketare.
Tace hakan ya nuna cewar ko da shike akan sayarwa kasashen na ketare makaman ne tare da sharadin kada ayi amfani dsu a yankuna dake fama da tashin hankali, amma babu wata hanya ta bincike ko tabbatar da ganin cewar kasashen da suka sayi makaman sun kiyaye wannan sharadi. A yanzu, kamfanin da zai sayar da makaman shi kadai ne ake bukatar yayi bayanin abin da za'a yi da wadannan makamai. Daga bangarenmu, ba'a gudanar da wani bincike a game da ko wadanda suka sayi wadannan makamai suna amfani dasu kan abinda suka sayi makaman saboda shi. Dangane da haka, mun ga yadda wasu kasashe suke daukar wannan mataki, mun kuma ga cewar idan muka kara maida hankali irin wannan bincike abu ne dake iya samuwa.
A daura da haka, Erich Fritz dan majalisar dokoki na jam'iyar CDU dake mulki yace a ra'ayinsa, irin wannan bincike kan kasashen da aka sayarwa makaman ba abu ne da zai yiwu ba, saboda hakan zai yi jagora ko wace shekara ga zaman majalisar dokoki domin muhawara kan tsaro da makamai, abin da zai sabawa manufofin kungiyar NJato da kungiyar hadink an Turai. Yace a yanzu ma, Jamus din kafin ta bada amincewar ta ga sayara wata kasa, takan yi nazarin manufofin kare hakkin yan Adam da tsaro a kasar dake son sayen makaman.
Mawallafi: Drechsel/Umaru Aliyu
Edita: Yahouza Sadissou