1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ägypten Muslimbruderschaft

February 4, 2011

Ƙungiyar 'Yan Uwa Musulmi da aka fi sani da Muslim Brothers a ƙasar Masar ta ce zata ba da goyan baya ga dukkan jam'iyyun da suka samu goyan baya daga al'uma.

Mohammed Mehdi Akef shugaban ƙungiyar 'yan uwa Musulmi a ƙasar MasarHoto: AP

Yau sama da kwanaki goma ke nan ana fama da zanga-zanga da neman shugaba Hosni Mubarak da yayi murabus daga kan karagar mulkin ƙasar Masar. A hukumance dai ƙasashen yammaci na iƙirarin ba da goyan baya ga samun canjin demokraɗiyya a ƙasar ta Masar, amma a ɗaya ɓangaren suna nuna fargabarsu game da komawar mulki zuwa ga hannun ƙungiyar nan ta 'yan uwa musulmi ko kuma Muslim Brothers a turance, wadda aka ce wai tana fafutukar kafa wata janhuriya ta Islama a ƙasar.

A idanun ƙasashen yammaci dai gwamnatin shugaba Hosni Mubarak a ƙasar Masar ta zama tamkar wata kafa ce dake hana wa masu tsananin kishin addini wata dama ta kama ragamar mulki. Amma fa a yanzu, sakamakon matsin lambar da Mubarak ke fuskanta ba ƙaƙƙautawa, ƙasashen na yammaci sun fara nuna tsoro game da yiwuwar mayar da ƙasar ta Masar ƙarƙashin mulkin Islama. To sai dai kuma Lutz Rogler, ƙwararren masani akan al'amuran Islama, ya ce wannan tsoron ba ya da tushe. Domin kuwa ita kanta ƙungiyar 'yan uwa Musulmi ta Muslim Brothers, wadda aka kafa ta tun shekaru 80 da suka wuce, tuni yanayinta ya canza:

"Ƙungiyar ta Muslim Brothers ba ƙungiya ce ta mayaƙa ba. Ta ƙunshi nau'in mutane dake da aƙidoji daban-daban. Bugu da ƙari kuma ƙungiyar ba ta ƙyamar shikashikan demokraɗiya ko haɗin kai da sauran 'yan adawa."

A shekara ta 1928 aka kafa ƙungiyar

A shekara ta 1928 ne dai Malamin makarantar faramare Hassan Al-Banna ya ƙirƙiro wannan ƙungiya a matsayin mai neman canji. Kuma manufarta ce ta ƙirƙiro wata al'uma mai girmama manufofin addinin musulunci. Sai bayan yaƙin duniya na biyu ne ƙungiyar ta rikiɗe domin ta ƙunshi kowa-da-kowa. A sakamakon wani harin ƙunar baƙin waken da aka kai kan tsofon shugaban ƙasar Masar Gamal Abannasser, wanda bai yi nasara ba, sai shugaban ya ba da umarnin rusheta a shekara ta 1954 aka kuma zartar da hukuncin kisa akan da yawa daga 'ya'yanta.

A wajejen ƙarshen shekarun 1970 ne ƙungiyar ta Muslim Brothers ta sake ɓilla fagen siyasa ta kuma wayi gari a matsayin wata ƙaƙƙarfan 'yar adawa. A baya ga kutsa kai a al'amuran siyasa, ƙungiyar kazalika, tana taimakawa wajen gina asibitoci da cibiyoyin kyautata jin daɗin rayuwar jama'a. Hakan ta sanya ta samu aarfan matsayi tsakanin talakawa 'yan rabbana ka wadata mu. Kuma ko da yake an haramta ta a matsayin wata jam'iyyar ta siyasa, amma ƙungiyar ta 'yan uwa musulmi tana ba da goyan ba ya ga 'yan takarar masu zaman kansu dake da kujera a majalisar dokokin Masar kuma ta haka ta samu kashi ɗaya bisa biyar na kujeru a majalisar dokokin ƙasar tun daga shekara ta 2005.

Ana damawa da ƙungiyar a zanga-zangar adawa


'Ya'yan ƙungiyar 'yan uwa Musulmi sun shiga ana damawa da su a zanga-zangar MasarHoto: AP

Ƙungiyar dai ta shiga ana damawa da ita a zanga-zangar neman demokraɗiyya da walwala a ƙasar Masar. A cikin sanarwar da ta bayar a hukumance ta ce adawar da ake yi da gwamnatin shugaba Mubarak ba wani juyin juya hali ne na Islama ba. Kuma Hilmi Daschasar, ɗaya daga cikin gaggan shuagabannin ƙungiyar ya musunta zargin da ake yi na cewar ƙungiyar na neman yin amfani da damar da ta samu ne a yanzun domin ƙwatar mulki:

"Ƙungiyar 'yan uwa musulmi na fatan ba da cikakken haɗin kai ne ga dukkan jam'iyyun da suka samu goyan baya daga jama'a a zaɓe, ya-alla 'yan gurguzu ne ko masu sassaucin ra'ayi da ragowarsu. Ta haka Masar zata nuna wa duniya tsantsar demokraɗiyya, wadda 'yan uwa musulmi zasu shiga a dama da su amma ba zasu yi babakere a cikinta ba."

Mawallafi: Nader Alsarras/Ahmad Tijani Lawal

Edita: Abdullahi Tanko Bala