Rawar da sojoji suka taka a siyayar Jamhuriyar Nijar
February 15, 2016 Hakikan talakawan kasar ta Nijar na ci gaba da daukan batun tsaro a matakin farko da suka kama duk shugaban da ya yi nasarar lashen zaben, ya kasance daya daga cikin alkawura abin cikawa da shugabannin suka dauka a yayin yakin neman zabe. Ganin irin yadda al'amura ke ci gaba da sukurkucewa, tare da saka dimbin jama'a cikin fargaba, ko da yake ma dai daya bayan daya 'yan takarar a duk taron ganawa da jama'a na ikirarin daukan lamarin tsaron da muhimmanci.
Baya ga irin rawar da ya taka da gwamnatinsa a shekarun da ya kwashe na jagoranci kasar shugaba Alhaji Mahamadou Issoufou, dan takaran shugabanci daga jam'iyyar PNDS Tarayya, a ranar farko ta kaddamar da yakin neman zaben sa a birnin Diffa cewa ya yi, batun tsaro shi ne kan gaba in ya sake lashe zabe, ko da yanzu ma gwamnatinsa ta rawar gani acewarsa.
Wannan batu na tsaro dai ba wai 'yan takaran shugabancin kasa kawai ya cinyewa tuwo a kwariya ba, amma hatta ga 'yan takaran majalisar dokoki daga jam'iyyu daban-daban, na yin tsokaci ta la'akari da irin yadda 'yan bindiga dadi ke cin karensu. A cewar Mustafa Ibrahim, wani matashin dan takara daga jam'iyyar CPR Inganci, daga mazabar Olelewa da ke daf da matatar man kasar ta Nijar, wanda ya yi Allah wadai da matsalolin tsaron da kasar ke fiskanta a halin yanzu.
Kawo yanzu dai jama'a sun zura ido kuma suna rubuta alkawuran da 'yan takarar ke dauka a rubuce, sabanin irin yadda a shekarun baya da suke sauraren al'kawuran kunnen kawai, yayin da yan siyasa ke gangami su bar jama'a a dandalin taron.