1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin yankin Sahel ya mamaye kanun jaridun Jamus

Mohammad Nasiru Awal
December 20, 2019

Yaki da tsageru masu dauke da makamai a yankin Sahel na Afirka gami da sabuwar yarjejeniyar zaman lafiyar Sudan ta Kudu na cikin abubuwan da suka mamaye jaridun Jamus.

Symbolbild- Nigera - Militärübung
Hoto: picture-alliance/dpa/P. de Poulpiquet

A wannan makon za mu sharhi da labaran jaridun na Jamus kan nahiyarmu ta Afirka da jaridar neue Zürcher Zeitung wanda ta yi sharhi kan yawan adawa da ake nunawa kasar Faransa a yankin Sahel, tana mai cewa zanga-zangar nuna kyama ga kasar Faransa a yankin na Sahel alama ce ta rashin samun biyan bukata na burin da aka sanya gaba. Jaridar ta ce yayin da Faransa ke cikin makokin sojojinta 13 da suka rasa ransu a kasar Mali karshen watan Nuwamba, da kuma miliyoyi dubba na kudi da ta kashe a aikin da sojojinta ke yi a yankin Sahel, kyamar kasar na karuwa a yankin, inda ake zargin kasar da rashin tabuka wani abin kirki a yakin da 'yan ta'adda.

Hoto: Getty Images/AFP/B. Hama

Jaridar ta ce adawa da Faransa da ke karuwa a kasashen da ta taba yi wa mulkin mallaka na zama wani fushi da ke karuwa a sabili da tsawon lokacin da wannan yaki ke dauka, kuma har yanzu ba wanda zai iya yin hasshen ranar karewarsa.

Sabuwar yarjejeniya da ke da zumar samar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu wannan shi ne taken labarin da jaridar Süddeutsche Zeitung ta buga tana mai mayar da hankali kan makomar kasar da ke zama sabuwa a jerin kasashen duniya kasancewa a shekarar 2011 ta samu 'yancin kanta daga kasar Sudan, amma ta tsunduma cikin yakin basasa shekaru biyu baya.

Hoto: Presidential Press Unit of Uganda

Jaridar ta ce yakin da ake yi da burin rike madafun iko da iko da arzikin kasa, ya yi sanadin rayukan dubun dubutan mutane sannan wasu miliyan hudu sun yi kaura. Amma a ranar Talata da ta gabata masu rikici da juna sun sanar da cimma sabuwar yarjejeniya da ta yi tanadin kafa gwamnatin hadin kan kasa kafin tsakiyar watan Fabrairu na shekara ta 2020. Jaridar ta ce wannan ba shi ne karo na farko da masu yakar juna suka cimma shirin zaman lafiya ba, amma watakila wannan na iya zama dama ta karshe ga kasar wadda a dole za ta fara gina kanta tun daga tushe.

Ita kuwa jaridar Die Tageszeitung a wannan makon ta leka kasar Yuganda ne tana mai cewa rashin aikin yi a cikin kasa, 'yan Yuganda kimanin dubu 150 na aiki a kasashen Gabas ta Tsakiya kamar yadda alkaluman ma'aikatar kwadagon kasar suka nunar. A shekara suna aikawa iyali da sauran dangi a gida miliyan 600 na dalar Amirka, wanda akasari ake amfani da kudaden a matsayin jari na kafa kamfani da a hannun daya ke samar da aikin yi a cikin Yugandar.

Hoto: DW/S. Schlindwein

Sai dai kasancewa kasar na daga cikin kasashen duniya da suka fi yawan haihuwa saboda haka tana fama da matsalar bunkasar jama'a cikin sauri, wanda hakan ke janyo matsalar rashin aiki. Shi yasa matasa ke barin kasar don nema aiki a ketare ta hanyar kamfanonin samar da aiki. Sai dai kuma masu safarar mutane ba bisa ka'ida ba sun shiga cikin harkar, abin da ya tilas gwamnati Yugandar soke lasisin da yawa daga cikin kamfanonin da ke samar da aiki ga 'yan Yuganda a kasashen na yakin Gabas ta Tsakiya.