1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ghana: Rawar matasa a babban zabe

December 5, 2024

Yayin da ake shirin zaben shugaban kasa a Ghana a Asabar din karshen mako wato bakwai ga wannan wata na Disamba da muke ciki, wacce rawa matasa za su taka a zaben?

GHana | Siyasa | Zabe | Shugaban Kasa | Mahamudu Bawumia | John Dramani Mahama
'Yantakarar shugaban kasar Ghana, Mahamudu Bawumia da John Dramani MahamaHoto: NIPAH DENNIS/AFP/Getty Images | OLYMPIA DE MAISMONT/AFP

Sama da matasa dubu 480 ne ake sa ran zasu kada kuri'a a karon farko, a babban zaben da  za a gudanar a karshen mako a kasar Ghana. Alkaluman Hukumar Zaben kasar ne suka tabbatar da adadin matasan, wadanda ake ganin za su iya taka rawar gani wajen fitar da wanda zai yi nasara a zaben shugaban kasa. A shekarun baya galibi matasan da ke kada kuri'unsu a karon farko kan bi ra'ayin iyayensu ne, ko kuma wata nasaba da suek da ita da wata jam'iyya ko dan takara. Sai dai a wannan karon ma kamar kowanne lokaci, akwai takaddama tsakanin mayan 'yan takarar shugabancin kasar biyu  da suka kasance Musulmi da Kirista. Sai dai kuma duk da yadda ake ganin siyasar Ghana na neman karkata zuwa ta addini, manyan 'yan takarar biyu dai sun mayar da hankali a gangamin yakin neman zabensu kan bunkasa harkokin ilimi da ma batun bayar da shi kyauta musamman ga matasa.