1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane da suka rasu a rikicin Burundi na karuwa

Yusuf BalaJune 17, 2015

Adadin mutane da suka rasu a zanga-zanagar adawa da shirin tazarce na shugaban kasar Burundi ya haure mutane 75 kamar yadda kungiyoyi da ke fafutikar kare hakkin bil Adama suka bayyana.

Burundi Proteste gegen Präsident Nkurunziza
Masu zanga-zanga a BurundiHoto: Reuters/G. Tomasevic

Wannan dai na zuwa ne daidai lokacin da masu adawa da tazarcen shugaba Pierre Nkurunziza a birnin Bujumbura ke kara azama a fafutikarsu.

An gusa da lokacin da ake son yin zaben 'yan majalisar wakilai a wannan kasa da ke a gabashin Afrika.

Su dai wadannan masu zanga-zanga da suka fantsama kan tituna tun daga ranar 26 ga watan Afrilu sun bayyana cewa neman tazarcen na shugaba Nkurunziza da ya tsallake wani yunkurin juyin mulki bai halatta ba.

Kasar dai ta Burundi ta tsara cewa nan gaba za a yi zaben 'yan majalisar dokokin kasa da na kananan hukumomi, wato a ranar 29 ga watan na Yuni yayin da zaben shugaban kasa zai zo a ranar 15 ga watan Yuli sanann ayi na 'yan majalisar dattawa ranar 24 ga watan na Yuli.