1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Iran ta kai hari kan Kurdawa

Ramatu Garba Baba
September 29, 2022

Mutum akalla 13 ciki har da wani dan kasar Amirka ne suka mutu a sakamakon wasu hare-hare da rundunar sojin Iran ta kai kan yankin Kurdawa a Iraki.

Mutane da dama sun mutu a hare-haren KurdistanHoto: Fariq Faraj/AA/picture alliance

A wata sanar da Ma'aikatar harkokin wajen Amirka ta fitar, ta ce, wani dan kasar na daga cikin wadanda suka mutu a sakamakon wasu jerin hare-hare da rokoki da rundunar sojin Iran ta kai a yankin Kurdistan na kasar Iraki. Sanarwar ta ce, ba za ta yi karin bayani kan harin a yanzu ba, saboda dalilai na tsaro.

Akalla mutane goma sha uku aka tabbatar sun salwanta a hare-haren da Iran ta kaddamar a yankunan da ta kira da sansanonin kungiyoyin abokan hamayyarta watau Kurdawa da ta zarga da hannu a goyon bayan zanga-zangar da ke gudana a yanzu haka a Tehran da sauran sassan kasar kan kisan matashiya Mahsa Amini.