Wane hali masu bukata ta musamman ke ciki a Kaduna?
December 3, 2025
Dokar da aka kaddamar a shekara ta 2021, a zamanin tsohon gwamnan Kaduna Malam Nasiru El-Rufai, doka ce mai ingancin shekaru goma, tana da matuƙar muhimmanci wajen ƙarfafa ’yancin masu bukata da kare kimarsu, tare da ba su dama daga dukkan fannoni, tun daga kasuwanci zuwa ilimi da aikace-aikace da ma tabbatar da cewa duk wani sabon gini ya tanadi hanyoyin da suka dace da su domin samun saukin shiga.
Kwamared Rilwanu Abdullahi, shugaban ƙungiyar masu bukata ta musamman ta ƙasa, ya bayyana cewa dokar tana da tasiri biyu da suka inganta rayuwar masu bukatar faɗin jihar. Ya ce shekaru 20 zuwa 30 da suka gabata babu wannan doka face batun koyon sana'a. Amma yanzu dokar ta taimaka wajen faɗaɗa nau'ukan ayyukan da za su inganta rayuwar masu bukatar ta musamman da ci gaban iliminsu.
A cikin shekaru huɗu da fara aiwatar da dokar, rayuwar masu bukata ta musamman a Kaduna ta fara sauyawa, musamman wajen ƙarfafa kananan yara masu lalura su samu ilimi, da kuma tabbatar da ɗaukar waɗanda suka kammala karatunsu a ayyukan gwamnati da na al'umma.
A irin wannan rana, hukumomi da ƙungiyoyin kare hakkin masu bukata na amfani da damar wajen wayar da kan jama’a a kan ’yancin masu bukata nta musamman.
Sai dai Malam Ishiyaku Ma’aji na haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu bukata ta musamman a jihar Kaduna, ya ce babban abin da suke son gani, shi ne tabbatar da cewa duk hukumomi da masu gine-gine suna bin ka’idojin dokar yadda ya kamata. Sannan akwai buƙatar yaba wa wasu kamfanoni bisa jajircewarsu wajen gudanar da ayyukan da suka dace domin inganta rayuwar masu bukata ta musamman a Kaduna.
Gwamnatin jihar ta Kaduna dai ta sake jaddada kudurinta na kare hakkin masu bukata ta musamman din, da kuma ci gaba da ƙirƙiro hanyoyin inganta ilimin yara masu samun kansu da wasu larurori.