1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Jiragen ruwan 'yan cirani na cikin hadari a teku

Ramatu Garba Baba
April 10, 2023

Ana kokarin ceto rayukan 'yan cirani fiye da dubu daya da suka makalle a wasu jiragen ruwa da ke fuskantar barazanar nutsewa a cikin tekun Bahar Rum.

Daruruwan 'yan cirani sun mutu a yunkurin shiga Turai
Daruruwan 'yan cirani sun mutu a yunkurin shiga Turai Hoto: Getty Images/AFP/T. Jawashi

Jami'an da ke aikin tsaron gabar ruwan kasar Italiya na gudanar da wani gagarumin aikin ceto rayukan 'yan cirani da ke cikin wasu jiragen ruwa da aka gano na fuskantar barazanar nutsewa a cikin tekun Bahar Rum. Mutum akalla dubu daya da dari biyu aka kiyasta na cikin jiragen da suka taso daga arewacin Libiya a kan hanyar shiga Turai.

Wata kungiyar mai zaman kanta ta kasar Jamus mai suna Sea-Watch International, wacce ta gano jiragen da taimakon fasahar zamani ta ce, an tura wa jiragen man fetur da ruwa, amma mahukuntan kasar Malta na kawo musu cikas a kokarin ceto mutanen. Kafin aukuwar lamarin na wannan Litinin, rahotanni na cewa, 'yan cirani kimanin dubu biyu aka ceto daga gabar ruwan Italiyan tun daga ranar Jumma'ar da ta gabata.