1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Karuwar 'yan gudun hijira a yankin Sahel

Gazali Abdou Tasawa AH
October 17, 2025

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD ta nuna damuwa a game da karuwar 'yan gudun hijira a yankin Sahel a sakamakon yaduwar ayyukan kungiyoyin 'yan ta'adda a wannan shekara ta 2025.

'Yan gudun hijira a Agades Nijar
'Yan gudun hijira a Agades NijarHoto: Kristin Palitza/dpa/picture alliance

Hukumar ta nuna wannan damuwa ce a cikin wani rahoton bincike da ta fitar inda kuma ta yi shelar neman agajin gaggawa ga kasashen duniya domin taimaka wa miliyoyin 'yan gudun hijirar musamman a kasashe mambobin kungiyar  AES Nijar Mali da Burkina Faso. 

Ranar 'yan gudun hijira ta duniya

02:03

This browser does not support the video element.

Rahoton hukumar kula da 'yan gudun Hijirar ta MDD ta HCR ya bayyana cewa yanzu haka akwai  'yan gudun hijira kimanin miliyan hudu da tashe-tashen hankula masu nasaba da ayyukan kungiyoyin 'yan an ta'adda suka raba da matsugunnansu a kasashen Burkina Faso, Mali , Nijar da kuma makobtansu.

'Yan gudun hijiraHoto: AP/picture alliance

Kuma kaso 80 cikin dari mata ne da kananan yara wadanda ke cikin hali na bukatar taimakon abinci da magungunan da muhallin zama. A kann haka ne hukumar ta MDD ta yi kira ga kasashen duniya da su gaggauta domin kuwa ya zuwa yanzu kaso 32 cikin dari ne kadai na kudi dalar Amurka miliyan kusan 410 da take bukata domin fuskantar matsalolin yankin na Sahel suka shigo hannunta. 

Rahoton hukumar ya nunar da cewa ya zuwa tsakiyar wannan shekara ta 2025, gidajen asibiti sama da 900 ne da makarantu dubu 14 da 800 matsalar tsaro ta tilasta rufe su a yankin na Sahel inda yara kimanin miliyan uku suka daina zuwa makaranta. 

'Yan gudun hijira Katsina sun shiga mawuyacin hali

02:28

This browser does not support the video element.

A jamhuriyar NijarJjihar Tillabery na daga cikin yankunan da suka fi fama da wannan matsala ta 'yan gudun hijira. 

Sahara motar 'yan gudun hijiraHoto: imago/CHROMORANGE

Kawo yanzu dai gwamnatin kasar Nijar ba ta ce uffan ba a game da wannan rahoto na hukumar ta  HCR wanda ya zo a daidai lokacin da rundunar sojin kasar ko baya ga fafatawa da 'yan ta'adda ta kaddamar da shirin taimaka wa al'ummomin wasu yankunan masu fama da matsalar tsaro da abinci da kuma magunguna. 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani