Rediyo na fuskantar barazanar fasahar zamani
February 14, 2021Sama da shekaru 110 ke nan da fara amfani da kafar rediyo a duniya domin isar da sako na fadakarwa ko nishadantar da al'umma. Daya daga cikin taken bikin ranar a bana, shi ne wajibcin rediyo na daukar sabbin fasahohin zamani domin cimma burin isowa ga al'umma.
Albarkacin ranar radio ta duniya wakilinmu na Kano Abdurrahman Kabir, ya duba mana ya duba mana ci gaban da Freedom Radio, gidan rediyo na farko mai zaman kansa a Kano ya samu ta wannan bangare.
Gidan rediyon na Freedom tun shekarun baya ya koma wannan tsari da duniya ke yayi a wannan zamani. Tun a bara kuma ya mallaki sashi da zai rika gane masa hanya ta bangaren zamanantar da shirye shirye-shiryensa a cewar shugaban tashar, Malam Ado Sa’idu Warawa.
Kasancewar a ko ina ana iya kama tashar ta kan internet kai tsaye ne ko ta sauraron shirye-shiryen da lokacin sauraronsu ya shude ko kuma samun labarai da dumi-dumi ko da ba a lokacinsu ba ne ya kara bai wa jama’a dama ta sanin abubuwan da suke bukatar ji ko gani a kan kari.
Aminu Uba Kulo da Ibrahim Mu’azu sun yi tsokaci da wani shiri wanda wanda ba ya wuce su tun bayan zamanantar da shirye-shiryensa.
A yanzu dai wannan sauyi da ya zamanantar da shirye-shirye rediyo ta intanet, ya kara karfafa hulda tsakanin tashar da manyan gidajen rediyon duniya musamman ta bangaren musayar shirye-shirye.