Donald Trump ne dan takarar Republican
July 17, 2024Dan takarar mai shekaru 78 a duniya, tsohon shugaban Amurkan Donald Trump da ya tsallake rijiya da baya a harin da aka kai masa ya sha tafi da sowa lokacin da aka bayyana shi a matsayin halastaccen dan takara da jam'iyyar Republican ta tsayar a babban taron da ta shafe kwanaki tana gudanarwa. Manyan masu adawa da Trump kamar Nikk Haley da gwamnan jihar Florida Ron DeSantis su goyi bayanTrump tare da ayyana kudurinsu na zama tsintsiya madaurinki daya, su kawar da Shugaba Joe Biden da jam'yyarsa ta Democrat daga fadar mulkin Amurka ta White House.
Suma sanatocin jam'iyar ta Republican ba a barsu a baya ba, inda Sanata Marco Rubio daga jihar Florida da shekara ta 2016 ya raba gari da Donald Trump ya kuma fito ya caccake shi ya nunar da cewa jam'iyyarsu ta dauki hanyar lashe zaben Amurka na bana ba tare da wani shamaki ba. Dan majalsar ta dattawa ya tunasar da al'ummar Amurka cewa, madugu ne ke jagorantar jam'iyyar Republican da yunkurin kisan gillar da aka yi masa a karshen mako bai sare masa gwiwa a kokarin da yake na sake dawo da martabar kasarsa ba. Iyalan Trump sun bayyanawa babban taron jam'iyyar ta adawa cewa, kafin yunkurin kashe shin a karshen mako a Pennsylvania, an sha aika musu sakonnin barazanar kisa tare da kokarin barbada musu hodar da ka iya hallaka su. Ana sa ran dan takarar mataimakin shugaban kasa J.D. Vance da aka nada cikin wannan makon zai yi jawabi ga 'yan jam'iyyar, yayin da Donald Trump zai rufe taron da jawabin rufe taro a ranar Alhamis din da ke tafe.