Rice zata zata kai ziyara Gabas Ta Tsakiya
July 21, 2006A dangane da mawuyacin hali na rashin sanin tabbas da aka shiga ciki a yankin na GTT, kwamitin sulhu na MDD yayi wani zama na musamman. Bayan taron sakatariyar harkokin wajen Amirka Condoleezza Rice ta sanar da cewa a ranar lahadi zata yi tattaki zuwa GTT a wani yunkurin gano bakin zaren warware wannan rikicin ta hanyoyin diplomasiya. Tace manufar ziyarar ita ce ganawa da shugabannin yankin da halartar wani taro a birnin Rom akan rikicin na GTT. Ita ma ma´aikatar harkokin wajen Jamus a birnin Berlin ta sanar da cewa ministan harkokin waje Frank Walter Steinmeier na shirin zuwa yankin na GTT, inda zai tattauna da shugabannin yankin don gano bakin zaren warware batakashin da ake yi tsakanin Isra´ila da Hisbollah a hannu daya da kuma Isra´ila da Hamas a daya hannun. A yau ma wato kwana 10 a jere Isra´ila ta ci-gaba da kai hare hare ta sama a Libanon yayin da Hisbollah kuma ta yi ta harba rokoki a arewacin Isra´ila. Yanzu haka dai an kwashe mutane fiye da dubu 100 daukacin su baki daga Libanon a cikin kwanaki kalilan da suka wuce.