1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Riek Machar ya ce bai shirya amincewa da tsagaita wuta ba

December 31, 2013

Amma duk da haka gwamnatin Sudan ta Kudu da kuma 'yan tawayen kasar sun amince su zauna kan teburin sulhu.

Hoto: Al-Haj/AFP/Getty Images

Yayin da ake kokarin tattaunawar zaman lafiya tsakanin bangarorin Sudan ta Kudu a birnin Addis Ababa na kasar Ethiopia, tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Machar ya tabbatar da cewa ba shi da wata aniya ta tsagaita wuta a wannan rikici, inda ya kara da cewa dakarun da ke goya masa baya na kan hanyar su ne ta zuwa Juba babban birnin kasar. Amma kuma duk da haka ya tabbatar da aike tashi tawaga ya zuwa birnin na Addis Ababa inda za a yi wannan tattaunawa. Sai dai dakarun gwamnatin kasar sun karyata batun kwace birnin Bor inda suka ce yanzu haka yana hannunsu. Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Dunia Ban Ki-moon ya sanar da cewa tashe-tashen hankulan na iya bazuwa ko ina cikin kasar ta Sudan ta Kudu dan haka ya yi kira da a zauna a kan teburin sasantawa domin warware rikicin. Daga nashi bangare shugaba Salva Kiir ya ce lalle za a zauna a tattauna amma bai san sakamakon tattaunawar ba.

Mawallafi: Salisou Boukari
Edita: Mohammad Nasiru Awal