1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Riek Machar ya fice daga Juba

Abdourahamane HassaneAugust 18, 2016

An ba da sanarwa cewar jagoran 'yan tawaye na Sudan ta Kudu Riek Mashar ya fice daga juba babban birnin kasar tun a cikin watan jiya.

Südsudan Riek Machar Rebellenführer
Hoto: picture-alliance/AP Photo/M. Ayene

Riek Machar ya fice ne sakamakon yadda aka dakatar da shirin sulhu na tattaunawa tsakanin gwamnatin da 'yan tawaye.Wasu na kusa da shugaban sun ce ya yi hijira a cikin wata kasa da ke a yankin gabashin Afirka inda ake da tabbacin tsaro lafiyarsa.
Tun farko jagoran 'yan adawar ya bukaci kwamitin sulhu na MDD ya tura wata runduna sojoji ta shiga tsakanin to sai dai shugaban Salva Kiir bai amince da haka ba.