Riek Machar ya isa Juba
October 31, 2018Talla
Madugun adawar Riek Machar, ya isa Juba babban birnin kasar ne inda a wannan Laraba ake bikin murnar cimma yarjejeniyar nan ta zaman lafiya tsakaninsa da Shugaba Salva Kiir.
Mr. Machar wanda ya bar birnin sama da shekaru biyun da suka gabata, ya koma ne bisa sharadin kama aikinsa na mataimakin shugaban kasa, kamar yadda yarjejeniyar da aka cima a watan jiya ta nunar.
Bangarorin masu gaba sun tabbatar da maida wuka kube ne a wani taron sulhu da aka yi a Addis Ababa na kasar Habasha, cikin watannin da suka gabata.
A baya dai an sha irin wannan yarjejeniya ba tare da nasara ba, a kokarin da ake yi na dawo da zaman lafiya a Sudan ta Kudun da yakin basasa ya kassara rayuwar akalla mutum miliyan hudu.