1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaddama tsakanin Falasdinu da Isra'ila

Abdourahamane Hassane
January 3, 2023

Ministan tsaron kasa na Isra'ila Itamar Ben Gvir ya kai ziyara a masallacin Al-aqasa, wuri mai tsarki da ke tsakiyar tashin hankali a gabashin Kudus.

Israel Jerusalem | Felsendom auf dem Tempelberg
Hoto: Ammar Awad/REUTERS

Ministan ya kai ziyarar ne duk da barazanar da Hamas da Falasdinu suka yi tun can da farko kafin ziyarar, Ziyarar ministan mai tsatsaurar ra'ayi ta janyo martanin mai zafi na bangarorin gwamnatin Falasdinu da Hamas. Ma'aikatar harkokin wajen Falasdinu ta fitar da wata sanarwa yin Allah wadai da ziyarar a masallacin na Al-Aqsa. Abin da ta kira da cewar tsokana ce. Masallacin da ke a birnin Kudus na cikin yankin Falasdinu wanda Isra'ila ta mamaye tun a shekarar ta 1967.