1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Rigimar Sudan da hannun Rasha a Mali sun shiga jaridun Jamus

October 22, 2021

Jaridun Jamus a wannan makon sun dubi batutuwan Afirka ne da suka shafi dambarwar mulki a kasar Sudan da rudanin da wasu manyan kasashen Turai suka shiga game da iko a Afirka, da ma wata sabuwar zanga-zanga a Swaziland.

Krise in Sudan Abdalla Hamdok
Hoto: AFP via Getty Images

A yau sharhunan jaridun Jamus kan nahiyar Afirka za mu fara ne da kasar Sudan, inda a labarinta jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung, ta ce an ga wani yanayi da ba a saba ganin sa ba, inda kwatsam dubban mutane suka taru suna bore a Khartoum. Dubban mutanen sun hau kan titunan babban birnin kasar ta Sudan suna yin kira ga sojoji da su kifar da gwamnati mai ci a yanzu. Mutanen dai sun kafa tantuna ne a harabar fadar shugaban kasa, suna yin Allah wadai da masu mulki, suna cewa shin sojoji na tare da al'umma ko kuma sun barmu cikin yunwa suna gaya burodi kawai. A bariya dai irin wannan zanga-zanga ta yi sanadin kifar da gwamnati Omar Al-Bashir, bayan kusan shekaru 30 yana mulki, yayin da boren ya yi kamari sai sojoji suka sanar da sauke shi daga mulki. To amma bisa ga dukkan alamu talakawan kasar bukatarsu ba ta biya ba, don haka yanzu suka dawo kan titi suna neman sojoji su kifar da gwamnati mai ci. Yanzu dai ana gudanar da mulkin gambiza ne tsakanin soja da farar hula a kasar ta Sudan.

Kasashen Yamma musamman manya a Tarayyar Turai, sun shiga rudani bisa kasashen da suka yi wa mulkin mallaka a Afirka. A cewar jaridar der Tagesspiegel, yanzu haka Jamus da Faransa sun kasa sanin inda za su bullo wa kasar Rasha wacce yanzu haka ta ke ba za fukafukanta a a nahiyar Afirka. Jaridar ta ce wai shin rundunar sojan Jamus za ta tsaya a kasar Mali ta yi aiki kafada-da-kafada tare da sojojin kasar Rasha a Mali, ko kuma za su fice daga kasar? Kasar Mali dai a kwanankin nan ta sa hannun bisa kwangilar dauko sojojin haya kimanin 1000 daga Rasha. Wannan abu ne da yanzu ya jefa babbar ayar tambaya a kasar Jamus, wacce ke da sojojinta da ke aikin wanzar da zaman lafiya a kasar Mali, ciki har da horar da sojojin Malin. Kasar Rasha dai ba ta yi wani bata lokaci ba kan jefa kafarta a kasar da arewacin Afirka.

Hoto: AFP/Getty Images

Ita kuwa jaridar die tageszeitung, ta yi sharhinta ne kan zanga-zangar kasar Swaziland. Jaridar ta ce ko da cike an kwan biyu ana zanga-zangar ganin bayan Sarki Mswati III, amma a yanzu lamarin ya yi kamari, inda daliban makarantu suka rufe azuzuwa suna hawa kan titi suna boren ganin an yi fatali da mulki sarautar. Abin da ya kara dagula boren da ake yi dai shi ne harbe wasu dalibai biyu har lahira da jami'an tsaro suka yi, don haka aka rufe makarantu aka yi boren goyon bayan daliban da aka kashe. 

Sai kuma Najeriya, inda jardiar Süddeutsche Zeitung, ta rubata labari kan mayar da kayan al'adun Benin wanda kasar Jamus ke shirin yi. Jaridar ta ce ma'aiktar harkokin wajen Jamus ta sanar da cewa daga tsakiyar shekara ta 2023, za a fara mayar da kayayyakin tahiri na Benin wadanda ke a wuraren yawon bude ido a fadin kasar Jamus. Dama dai kayayyakin da turawan mulkin mallaka suka dauko a Benin da ke Najeriya, kamar sauran wanda aka kwaso a wasu kasashen, yanzu suna nan ajiye a dakunan adana kayan tarihi daba-daban da ke kasar ta Jamus, amma bisa matsin lamba musamman daga ofishin jakadancin Najeriya da ke Berlin, a yanzu an kammala yarjejeniyar mayar wa Najeriya kayan na Tarihi. Kafin dai a mayar da kayayyakin sai an gina sabon dakin ajiye kayan tarihi a birnin Benin da ke Najeriya, wanda za a gina bisa tallafin kasar ta Jamus don tabbatar da wurinalkinta kayakin tarihin.