Rigingimu a birnin Umuahia na Abia
September 14, 2017
Yanzu halin da ake ciki shi ne babu wata harka da ke gudana, domin shaguna da tituna da masanantu da ma'aikatu kamar an yi shara, illa dai za kai ta ganin jamaa na ta gujegujen Neman mafaka,inda Su kuma yan Biafra na Kungiyar IPOB ke ci gaba da takalar Sojoji tare da tirjiya nan da can.
Wani Mr Ogbonnaya Ikokwu, dan harida ne a Jahar ta Abia inda sabon rikicin ya barke:
Ya ce "tashin hankalin ya dauki wani sabon salo na dagulewa, domin nan da nake magana hedikwatar 'yan sanda na jahar Abia ne, kuma ko'ina ka duba jami'an tsaron 'yan sanda da soji kake gani, kuma yanzu aka bundige wasu mutane a daura da fadar gwamnatin jahar. Sannan kowa ka gani a dimauce yake ya na neman mafaka, haka kuma an kone wani ofishin 'yan sanda da ke kasuwar kasa da kasa ta Ariaria da ke Aba"
A wannan larabar dai an gudanar da wani taron maslaha, inda sarakunan gargajiya da gwamnan jaha da kuma kwamandan rundunar soji da ke shiyya ta 82 domin samun matsayarwarware wannan rikici.