1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

090111 süd-sudan referendum

January 10, 2011

Zaɓen raba gardama da ke ci gaba da gudana a yankin kudancin Sudan ya fara gamuwa da ƙalubale, sakamakon tashin-tashina da aka fiskanta tsakanin ɓangarorin yankin da ke gaba da juna.

'Yan kudancin Sudan ɗauke da makamaiHoto: DW/Schlindwein

Shugaba El-bashir ya yi imanin cewa yankin kudancin Sudan bai cancanci samun 'yancin cin gashin kai ba, saboda ɗimbin ƙalubale da ya ke fama da shi ciki har da na 'yan tawaye. A saboda haka ne fadar mulki ta Khartum ba ta yi mamakin jerin rigingimu da aka fiskanta a matakin farko na yunƙurin samar da 'yantacciyar Kudancin Sudan ba. Hasalima dai, faɗar ƙabilanci da ya wakana tsakanin ɓangarorin da ba sa ga macici da juna, da dama yankin yayi ƙaurin suna a kai, ya fara awan gaba da mutane takwas. Kana 'yan tawayen yankin da suka lashi takobin ci gaba da gudanar da yaƙin sunƙuru sun ci gaba da fafatawa da dakarun da ke biyeyya ga gwamantin Sudan. Daɗin daɗawa ma dai, wani abu da ake kyautata zato cewa bam ne ya tashi a Abyei da kan iyakar kudanci da kuma arewacin Sudan.

"'Yancin cin gashin kai na da mahimmaci a idanunmu"

'yan kudancin Sudan a runfar zaɓe a birnin Nairobi na KenyaHoto: dapd

Galibin 'yan yankin kudancin na Sudan na ci gaba da kafewa a kan bukatar dara ƙasar gida biyu, saboda baƙar azaba da suka fiskanta a lokacin da suka kasance tsinttsiya maɗaurinki ɗaya. Shekaru 20 suka shafe a cikin yaƙin basasa da ya salwantar da rayukan mutane da dama, yayin da wasu kimanin miliyon uku suka guje wa matsugunansu. Kazalika ba wasu ababen more rayuwa da gwamantin tsakiya ta samar musu tun bayan kafuwar ƙasar da ta fi faɗi a nahiyar Afirka. A saboda hake ne shugaban na Kudancin Sudan wato Salva Kiir ya ke ci gaba da jan hankali nesa domin a samu biyan bukata cikin sauƙi.

"Ina kira ga kowa da kowa da mu ƙara haƙuri, domin kuwa mun kusa shan romonsa. Ba abin da zai sa mu kai gaci na samun 'yanci illa kaɗa ƙuri'a"

'Yan kudancin sudan suka ce babu gudu babu ja da baya

'yan kudancin Sudan miliyon huɗu zuwa biyar da suka yi rejista na ci gaba da kaɗa kuri'insu a yankinsu na asali, da ma dai wasu ƙasashe na ciki da wajen Afirka ciki har da Kenya, a zaɓen da ake kyautata zato zai kai ga samar da kudancin Sudan mai cin gashin kanta. Bayanan da ke zuwa kama daga Juba da ke zama babban birnin kudancin sudan sun nunar da cewa jama'a sun fito ƙwan su da ƙwarƙwatan su domin tabbatar da cewa sun kaɗa ƙuri'ar da wasu ke dangantawa da na neman 'yanci. Wata mace ta bayyana farin cikinta a kafin ta samu damar kaɗa ƙuri'arta.

Shugaba Salva Kiir na kudancin Sudan bayan kaɗa ƙuri'aHoto: AP

" wannan rana ce ta musamman a garemu. Rana ce da za ta ba mu damar karrama mutane miliyon biyu da yaƙin basasa ya salwantar da rayukansu. Rana ce ta ɗora kudancin Sudan kan sabuwar alƙibla."

Wa'adin fitar da sakamakaon zaɓen raba gardama

Makwani biyar za a shafe ana tattara ƙuri'u tare da tantancesu kafin a sanar da sakamakon zaɓen raba gardama. Tuni ma dai wasu ƙasashen yammacin duniya ciki kuwa har da Amirka suka yi alkawarin taimaka wa kudancin Sudan tsayawa akan ƙafafunta idan 'yayanta suka amince ta zama ƙasa mai cin gashin kanta.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Yahouza Sadissou