1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rigingimun siyasa na ci gaba da janyo mutuwar jama'a a Kenya

January 10, 2013

A yayinda Kenya ke shirin gudanar da zaben shugaban kasa da na majalisar dokoki a ranar 14 ga watan Maris, tabarbarewar harkokin tsaro na barazana ga zabukan.

Kenyan police patrol past smoldering houses that had been burned in the village of Nduru, following renewed clashes between farmers and herders in the Tana River delta area of southeastern Kenya, Tuesday, Sept. 11, 2012. An official says armed raiders killed four people in Kenya's southeast despite a dusk-to-dawn curfew to prevent further clashes between the Orma and Pokomo tribes that have left more than 100 people dead. (Foto:AP/dapd)
Hoto: dapd

Kasar Kenya dai tana da kabilu hudu a cikinta amma biyu daga cikinsu ne ke da tasiri sosai kuma su ne manyan kabilun kasar. waton kabilar Pokoma da asalin su masunta ne da kuma kabilar Orma makiyaya da Manoma. Wadannan kabilu biyu kuma ne aka fi samun su da fadace-fadacen da yaki ci yaki cinyewa, abinda kuwa ke da nasaba da kabilanci, da mallakar filaye da kuma kogin Tana .

Akasari yankunan da ke a gabar kogin Tana na fama da fari da rashin kyawun yanayin da a sakamakon hakan kabilun biyu ke cigaba da halaka juna domin mallakar kogin.

A halin da ake cikin yanzu dai a kasar ta Kenya gwamnatin ta dukufa ka'in da na'in ga cigaba da shirye-shiryen gudanar da zaben a yayinda kuma wasu al'ummar kasar suka fara zargin wasu jami'an gwamnati da hannu dumu-dumu a cikin tashe-tashen hankulan domin cimma manufofin su na siyasa kamar yadda Kimani Njogu mai sharhi game da harkokin siyasa a kasar Kenya ya yi bayyani.....

Ya ce: "Kasar bata da kwararrun Shugabanni, sai ka samu mutane suna neman shugabanci ba don cigaban talakawan kasa ba amma domin son kai da kuma cimma bururrukan su. Lokaci yayi daya kamata mu tantance 'yan siyasan da ke kirkiro fadace-fadace na kabilanci da rarraba kawunan al'umman kasa. Mu zabi shugabanni na gari masu kishin kasa."

Kogin TanaHoto: dapd

Tushen rikicin gabar kogin Tana

Ko da yake wannan lamari ba sabon labari bane domin an kwashe shekaru da dama ana fama da kai wa juna hari tsakanin wadannan kabilu, inda ma a tsakanin shekara ta 2007 zuwa 2008 aka gwabza fada mai tsanani a tsakanin kabilun, daya yi sanadiyyar mutane 118 suka riga mu gidan gaskiya.

A wata sabuwar kuma, a wannan Alhamis (10. 01.13) mayakan kabilar Orma sun kai wa kabilar Pokoma hari da ya yi sanadiyyar kashe mutane 10.

Hassan Musa jami'in kungiyar Agaji ta Red Cross ne dake a yankin Tana ya ce harin ya janyo zaman dar-dar a yankin:

Ya ce: "Ana zama na rashin tabbas ko mu ma mun fara jin

tsoro. Yanzu harin fa kai-da-kai ne, kuma bamu yi tsammanin abin ya kai ga wannan matsayin ba. Hakan kuma na kara yawan mutanen da ke bukatar agaji daga gare mu. Muna dai kira ga shugabanni da su yi kokarin kirkiro da hanyar dakile wannan matsala."

Shugaba Kibaki da firayiminista Odinga na KenyaHoto: TONY KARUMBA/AFP/Getty Images

Mafita ga rigingimun kasar Kenya

To ayar tambaya da kuma wasu masanan ke dasawa game da wannan lamari shi ne, me ke hana gwamnatin kasar hukunta wasu jami'an gwamnatin da ke marawa kabilun baya? abinda kuwa wasu 'yan kasar suka fara yiwa lamarin kallon akwai lauje a cikin nadi.

Ko tantama babu gwamnatin Kenya tana da babban kalubale a gabanta na tabarbarewar tsaro domin yanzu haka ana zaman ne na dar-dar a kasar kuma bayan yankin Tana, yankuna kamar su Garissa, Samburu,Turkana, Moyale da kuma Isiolo duk na fama da fadace-fadace na kabilanci masu tsanani.

Mawallafiya : Mariam Mohammed Sissy
Edita : Saleh Umar Saleh