1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridun Jamus: Rikice-rikice a Afirka

Lateefa Mustapha Ja'afar
October 28, 2022

Rikice-rikicen da kasashen Mali da Habasha da kuma Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ke fama da su, sun dauki hankulan jaridun Jamus

Mali | MINUSMA | Hare-Hare | UNPOL | Bundeswehr
Rundunar MINUSMA a Mali na cikin hadariHoto: Nicolas Remene/Le Pictorium/IMAGO

Jaridar Süddeutsche Zeitung ta yi sharhinta mai taken: "Shawara mai matukar muhimmanci" Jaridar ta ce ta'addanci da mace-mace sun zama jiki a Mali, ya kamata sojojin Jamus su tabbatar da tasaro a kasar. Ga Rundunar Wanzar da Zaman Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Malin wato MINUSMA, rayuwa ce mai cike da hadari fiye da kowanne lokaci. Zuwa yaushe 'yan siyasa za su bari hakan ya ci gaba da faruwa? Ta ce a wannan makon ma, bayanan da suka fito daga Mali ba masu dadi ba ne. Jami'an rundunar Wanzar da Zaman Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Malin MINUSMA hudu sun rasa rayukansu, ciki har da sojan Jamus na rundunar Bundeswehr sakamakon wani bam da aka dana musu a boye. Suna daga cikin sojojin da ke Chadi, kuma suna kan hanyarsu ne ta zuwa Kidal da ke arewacin Malin. Ko da a kwanakin baya-bayan nan ma, sai da 'yan ta'addan masu ikirarin jihadi suka kai wani hari a tsakiyar kasar ta Mali tare da kashe mutane 11 yayin da wasu 53 kuma suka samu munanan raunuka.

Daruruwan mutane sun tsere daga gidajensu, sakamakon rikici a HabashaHoto: Shewangizaw Wgayehu/DW

Tattaunawa ta farko kan zaman lafiya a Habasha, in ji jaridar die tageszeitung tana mai cewa: Yaki tsakanin mayakan yankin Tigray da gwamnatin Habasha ya yi sanadiyyar asarar rayuka da dama. Duka bangarorin biyu na fuskantar matsin lamba kan su shiga tattaunawar sulhu. Jaridar ta ce a karon farko tun bayan da yaki ya barke a yankin Tigray da ke arewacin Habasha na kusan tsawon shekaru biyu, bangaren gwamnati da na mayakan yankin za su zauna tare a kan teburin sulhu. Duka bangarorin biyu sun bayar da tabbacin cewa wakilansu sun kama hanyar zuwa Afirka ta Kudu, inda tattaunawar sulhun za ta gudana karkashin jagorancin kungiyar Tarayyar Afirka AU. Ana dai iya cewa wannan shi ne fada mafi muni da ya janyo asarar rayuka a duniya, inda gwamnatin Amirka ta bayyana cewa kimanin mutane dubu 500 ne suka halaka tun bayan barkewar rikici tsakanin bangarorin biyu a watan Nuwambar 2020. Mafi yawansu yunwa ce ta halaka su, sakamakon toshe hanyar kai daukin abinci da gwamnatin Habashan ta yi ga yankin na Tigray. Rahotanni sun nunar da cewa, shi kansa yakin ya lakume rayukan kimanin mutane dubu 100 tun daga karshen watan Agusta. A hannu guda kuma sojojin gwamnatin makwabciyar kasa Iritiriya sun shiga tsundum cikin yakin, inda suke taimakon dakarun gwamnatin Habasha a hare-haren da suke kai wa kan mayakan na Tigray.

Karuwar 'yan gudun hijira, sakamakon rikici a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango Hoto: Jack Taylor/Getty Images

A wani sharhi na dabam da ta yi, jaridar ta die tageszeitung cewa ta yi: "Tserewa sabon rikici a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, dakarun gwamnati na son sake kwato iko da kan iyakar Bunagana da ke da matukar muhimmanci da kuma ke hannun 'yan tawayen M23 kafin duba yiwuwar tattaunawa da su. Tun a ranar Alhamis din da ta gabata, sabon fada ya barke a Bunagana da ke kan iyakar Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwangon da kasashen Ruwanda da Yuganda. Wannan dai ya tilasta mazauna garin na Bunagana tserewa zuwa makwabciyar kasa Yuganda. Rahotanni sun nunar da cewa, karo na hudu ke nan cikin wannan shekara da mazauna garin ke yin hijira. Ministan kula da 'yan gudun hijira na Yuganda, ya ce akwai kimanin mutane dubu takwas da a yanzu haka suke neman mafaka a Yugandan daga Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwangon.

Kamfanin BioNTech a Kigali fadar gwamnatin RuwandaHoto: Luke Dray/Getty Images

Jaridar Die Welt kuwa a nata sharhin mai taken mRNA-allurar riga-kafin cutar zazzabin cizon sauro wato Malaria da kuma tarin fuka. BioNTech na shirin kafa kamfanin samar da allurar a Afirka. Duk da cewa har kawo yanzu batun samar da allurar riga-kafin na a matakin farko, kamfanin na BioNTech na farko a Afirka da ke Kigali fadar gwamnatin kasar Ruwanda zai fara aiki ba da jimawa ba tare da samar da allurar riga-kafin cutar zazzabin cizon sauro wato Malaria da kuma tarin fuka samfurin mRNA. Ana sa ran fara samar da allurar a shekara ta 2024, inda baya ga allurar riga-kafin annobar COVID-19 kamfanin zai samar da allurar ta mRNA domin a amince da ita.