Jawabin shugaban gwamnatin Jamus na shiga sabuwar shekara
December 31, 2023A cikin sakonsa na shiga sabuwar shekara ga al'ummar Jamus, shugaban gwamnati Olaf Scholz, ya tabbatar da cewa rigin-gimun da duniya ke ciki na da matukar daukar hankali, amma kuma duk da hakan Jamus ba za ta yi sanyi a gwiwa ba, domin za ta samu mafita.
Shugaban gwamnatin kasar Olaf Scholz, ya bayyan cewa "Wahalhalu na karuwa, zubar jini na yawa, duniyarmu ta kasance mai cike da kalubale daban-daban da ke caccanzawa cikin hanzari irin na ban al'ajabi, ga wasu, wadannan abubuwan fargaba ne, to amma yana da kyau mu sauya dabi'unmu, ina kuma da yakinin cewa za mu samu mafita."
Shugaban gwamnatin ya kuma tabo batutuwan da suka shafi tattalin arziki da zamantakewa, inda ya ce an samu raguwar hauhawan farashin kayayaki, a yayin da albashi da kudin fansho suka karu, kana kasar ta yi tanadin wadataccen makamashin da zai bata damar tinkarar sanyin hunturu na bana.