1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bangui: Sama da mutane 10 sun halaka

Lateefa Mustapha Ja'afar
December 26, 2019

Sama da mutane 10 ne suka rasa rayukansu sakamakon wata arangama tsakanin tsageru masu dauke da makamai da 'yan kasuwa a Bangui babban birnin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Zentralafrikanische Republik Bangui MINUSCA UN Truppen
Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya MINUSCA a Jamhuriyar Afirka ta TsakiyaHoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Wata majiya ta jami'an tsaro ta nunar da cewa mutane 11 zuwa ne 14 suka rasa rayukansu bayan da rikicin ya barke da yammacin ranar Larabar da ta gabata. A nasa bangaren  wani limami mai suna Awad Al Karim ya nunar da cewa an kai gawarwaki 16 zuwa masallacin Ali Babolo da ke yankin, yana mai cewa rikicin ya barke ne bayan da 'yan kasuwar yankin PK5 da Musulmi ke da rinjaye suka dauki makamai, domin nuna adawarsu da harajin da tsagerun da ke rike da makaman suka sanya. Wani dan jarida da ke aiki da kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP da ke makwabtaka da yankin, ya ruwaito cewa an ji karar harbe-harbe da abubuwa masu fashewa a yammacin Laraba da wayewar garin Alhamis. A jawabinsa, kakakin rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a kasar MINUSCA Bili Aminou Alao ya nunar da cewa sun tura dakarunsu zuwa wajen da rikicin ya barke domin dawo da zaman lafiya.