1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Rikice-rikice

Kwango: Rikicin gwamnati da kungiyar M23

October 27, 2022

Wani kazamin fada ya sake barkewa tsakanin mayakan tawayen kungiyar nan ta M23 da kuma dakarun gwamnatin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, a yankin gabashin kasar mai fama da rikici.

Rikici | Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango | M23 | Fafatawa
Dakarun gwamnati da na 'yan tawayen M23 sun saba fafatawa a KwangoHoto: Arlette Bashizi/AFP/Getty Images

Fadan dai ya barke ne a wuraren da ke da arzikin ma'adinai, inda rahotanni daga garin Goma da ke arewacin lardin Kivu mai arzikin albarkatun kasa da suka hada da lu'u-lu'u da zinare da tagulla ke cewa sabon rikicin ya daidaita al'umomi da dama a yankin. Kimanin mutane dubu 23 ne suka tsere daga gidajensu ciki har da wasu dubu biyu da 500 din da tuni suka shige cikin kasar Yuganda, a cewar hukumar agaji ta Majalisar Dinkin Duniya. Leonard Ndume ya tsere  daga Tamugenga da ke zaman kauyensu na asali a kafa tare da 'ya'yansa 12 zuwa garin Kanyarushinya na Yuganda, duk dai a kokarin ganin sun yi nesa da hadarin da ke yakunansu na Kwangon.

Daruruwan mutane na tserewa daga gidajensu, a Jamhuriyar Dimukuradiyyar KwangoHoto: Guerchom Ndebo/AFP/Getty Images

Tun a ranar 20 ga wannan wata na Oktoba da muke ciki ne dai, 'yan tawayen na M23 suka kaddamar da sababbin hare-hare a kan sansanonin sojojin Kwangon a garuruwan Rangira-Rwanguba da Tchegerero. Wani mai aikin sa kai da ke shugabantar 'yan hijira a sansaninsu da ke Kanyarushinya Theo Musekura ya ce, ya zuwa yanzu ya karbi iyalan da ba su gaza 30 ba. Ya kuma nuna fargabar cewa, halin da mutanen ke ciki na iya kara muni. Kungiyar 'yan tawayen M23 da ta kafu a 2013 karkashin jagorancin sojojin kasar, ta kunshi tsofaffin sojojin Kwangon ne da suka balle a 2012 suka hadu domin turjiya ga gwamnatin kasar. Tun cikin watan Maris na wannan shekarar ne dai, suke ta tsananta hare-hare a kan fararen hula da ma wasu cibiyoyin sojojin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwangon da ke yankin gabashin Afirka.