1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici a kudancin Sudan

April 24, 2011

Ana ci gaba da fuskantar tashe tashen hankula a kudancin Sudan gabanin lafa 'yantacciyar ƙasa a watan Yuli

Sojan 'yan tawayen SPLA na kasar SudanHoto: dpa

A kudancin Sudan aƙalla mutane 55 cikinsu har da sojoji da farar hula sun rasa rayukansu a cikin faɗan da aka gwabza tsakanin dakarun gwamnati da 'yan tawaye. Wannan faɗa shi ne na baya-bayan nan a cikin jerin tashe-tashen hankula da ake fama da su a wannan yanki kafin samun 'yancin cin gashin kai a watan yuli. Tun sanda aka yi zaɓen raba gardama a wannan yanki mai arziƙin man fetur domin kafa 'yantacciyar ƙasa a watan janairu ne dai ake fama da tashe-tashen hankula. Sojojin SPLA na kudancin Sudan suna yaƙi ne da aƙalla ƙungiyoyin 'yan tawaye guda bakwai. Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙiyasce cewa mutane 800 suka rasa rayukansu a rikice rikicen ƙabilanci a wannan shekara a baya ga kuma wasu su dubbai da suka rasa gidajensu.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Abdullahi Tanko Bala