Rikici a Pakistan.
July 4, 2007A ƙalla almajirai dubu 9, yan shekaru 10 zuwa 20, ke karatu a cikin massalacin na Alal Massajid da aki sani da sunan jan massalaci, wanda kuma ke tsakiyar birnin Islamabad na ƙasar Pakistan.
Rikici a harabar wannna masalaci ya soma tun wattani kamar 3 da su ka wuce to amma sai ranar talata da ta wuce al´amarin ya yi tsamari, bayan da a ka yi fito na fito, tsakanin almajiran da jami´na tsaro, wanda a sakamkon hakan, mutane 16 su ka rasa rayuka, wasu kuma da dama su ka ji mummunan raunuka.
A yau rikicin ya ɗauki wani saban sallo, bayan da gwamnati ta kafa dokar ta ɓace a kewayem masalacin ta kuma jibge dakarun tsaro.
Gwamnatin na zargin almajiran da ke karatu a cikin masalacin, da aikata ayukan ta´adanci tare da taimakon yan taliban.
Ta yi kira gare su, su hita daga masalaci, su kuma ajje makamai ,kamar yadda ministan harakokin cikin gigan Afghanistan ya bayyana.
„ Za mu yi afuwa ga dukan wanda su ka yi kaka gida a cikin masalaci, da zaran su ka fita su ka kuma miƙa makaman da su ke dauke da su.
Sannan mu na fata za su bada haɗin kai domin tantance wanda su ka samar masu da makaman, da su ka yi anfani da su wajen kissan jama´ar da ba ta san hawa ba, balle sauka.“
Jim kaɗan bayan wannan kira, kimanin almajirai ɗari 7 su ka bada kai bori ya hau.
Dukkan wanda su ka fitan, sun samu tallafi take, daga gwamnati na kuɗi Euro 60, wato kimanin CFA jikka 40, kokuma Naira dubu 10 da yan ka.
To saidai a yanzu haka, akwai sauran wasu dubbunai, almajiran,wanda su ka ce, sai sun ga abinda ya ture wa buzu naɗi.
A cewar , wanda ya yi zama matsayin mai kulla da massalaci shawara da wannan matasa su ka yanke ta yi daidai domin abun da tura kusu wuta ya fi wuta zafi.
„Duk wanda ya tsinci kansa cikin halin mamaya, musulunci ya hore shi, ya tashi tsaye tsayin daka ,ya kare kan sa da kann sa.
A game da haka, matakin da wannan matasa, su ka ɗauka ya yi daidai, domin su na gudanar da ayuka, ne irin na yan taliban a ƙasar Afghanistan.
Su shinga matsayin jihadi domin kariya daga sojojin mamaye na ƙasa da ƙasa, wanda su ka ka yi kaka gida a Afghanistan da Irak ba tare da da hujja ba“.
Wannan saban rikici ya sa shugaban ƙasar Pakistan Pervez Musharaf a cikinwani hali natsaka mai wuya.
Bayan rigingimun da ya ke fuskanta na ci gida, ƙasashen turai da Amurika, na zargin sa, da nuna sako sako, ga almajiran na Lal Massajid.