Rikici a Rivers yayin zaben gwamnoni
April 11, 2015 Gabanin fara wannan tashin hankali dai tun daren jiya, wata sanarwa daga Abuja, ta bada Umarnin dakatar da AIG Tunde Ogunshaki, mai kula da shiyar 'yan sandan Najeriya ta shida, da kada ya sa baki a zaben jihar ta Rivers, inda aka umarce shi da ya kakkabe hannayensa daga al'ammuran zaben jahar da za'a gudanar yau dinnan.
Wannan umarni da aka nunar ya zo daga sama, wato fadar gwamnatin Najeriya da ke Abuja, kuma cikin dare aka bada ita, ta zo ne jim kadan bayan ganawar da mataimakin sifeto janar a shiyya ta shida, ya yi da wakilin DW a yankin Niger Delta Muhammad Bello, inda ya bayyana aniyar rundunar tsaron gamayya da ya ke jagoranta, wajen ganin zaben na jihar Rivers ya gudana ba tare da nuku-nuku ba.
Yanzu dai jama'a da dama na ta mamakin yadda hukumar zabe ta Najeriya wajen daukar matakin sauya wa shugabar hukumar zabe ta jahar Rivers wajen aiki, sakamakon koke koke da ga ciki da wajen Najeriya, da kuma zanga-zangar da jamiyyu suka dinga yi a jahar, dama a Abuja. Don gudin kada a zargi hukumar INEC ta zabe ta kasa, sai kwatsam awowi kadan za a fara zaben gashi an dauke mataimakin sifeton yan sanda Ogunshaki.