1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici akan makomar tsohon shugaban Masar

July 28, 2011

Hukumomin Masar sun miƙa wuya ga buƙatar masu zanga-zanga dangane da shari'ar Hosni Mubarak

Tsohon shugaban Masar Hosni MubarakHoto: picture-alliance/dpa

Kamfanin dillancin labaran ƙasar Masar ya sanar da cewar a ranar ukku ga watan Agustan dake kamawa ne za'a gudanar da shari'ar tsohon shugaban ƙasar Hosni Mubarak a birnin alQahira na ƙasar. Tsohon shugaban, wanda zanga-zangar neman sauyin ta tilasta masa sauka daga mulki, yana kwance ne a gadon asibiti dake birnin Sharm el-Sheikh, inda yake karɓar jiyyar da ta shafi bugun zuciya.

Sauya masa wurin shari'a zuwa birnin na alQahira, na daga cikin manyan buƙatun masu zanga-zangar da ta samar da juyin juya hali a ƙasar, waɗanda suke zaman doya da manja da hukumomin sojin dake tafiyar da harkokin mulki a ƙasar bayan hambarar da shugaban, wanda ya haɗa da zargin da suke yiwa sojojin cewar suna jinkirta gurfanar da tsoffin jami'an gwamnatin ƙasar.

Tsohon shugaba Mubarak - mai shekaru 83 da haihuwa dai zai fuskanci shari'a ne tare da 'ya'yan sa guda biyu, da kuma tsohon ministan kula da harkokin cikin gida a ƙasar Habib al-Adli, waɗanda ke jiran shari'a a wani gidan yarin dake birnin na alQahira.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Ahmad Tijani Lawal