1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici na lakume rayuka a Togo

Yusuf Bala Nayaya
December 10, 2018

An dai harbe mutum guda har lahira yayin da dayan kuwa bayan duka da ya sha aka jefa shi cikin wuta, bayan da fada ya barke a karshen mako da ya gabata a kasar ta Togo.

Belgien Togo Protest
Hoto: DW/J. C. Abalo

Mutane biyu ne suka rasu kawo wannan rana ta Litinin a yankin Sokode da ke zama babbar cibiya ta 'yan adawa a tsakiyar kasar Togo yayin da ake ci gaba da ba ta kashi tsakanin jami'an tsaro da 'yan adawa kamar yadda majiyoyi suka shedar.

An dai harbe mutum guda har lahira yayin da dayan kuwa bayan duka da ya sha aka jefa shi cikin wuta bayan da fada ya barke a karshen mako da ya gabata gabannin zaben 'yan majalisa da a ka tsara yi nan gaba cikin wannan wata.

A cewar Ouro Akpo Tchagnaou, da ke zama dan majalisa bangaren adawa daga jami'iyyar ANC 'yan sanda sun rufe tituna an kuma nemi yara kanana su koma gida bayan da aka shiga rudani, yayin da matasa suka shiga rufe hanyoyi da tarkace.