Rikici na ci gaba da tsananta a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, kwanaki hudu gabanin gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa.
Talla
Yanzu haka dai, ana gwabza fada tsakanin kungiyoyin tawaye da dakarun gwamnati da na Majalisar Dinkin Duniya a birnin Bambari da ke tsakiyar kasar. Tuni dai 'yan adawar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiyar suka bukaci da a dage zabe, yayin da al'ummar kasar da ma kasashe makwabta ke nuna fargaba dangane da tashe-tashen hankulan. Sa'o'i da dama aka shafe ana arangama tsakanin kungiyoyin tawayen da dakarun gwamnati a garin na Bambari da ke da tazarar kilometa 380 da Bangui babba birnin kasar.
Hasali ma garin da ke zama na hudu a girma, sai da ya fada hannun masu tayar da kayar baya, kafin dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a kasar su sake kwato shi. Ko da yake dai rundunar kiyaye zaman lafiyar ta MINUSCA ta bayyana cewa kura ta lafa a garin na Bambari, amma a garin Bossambele da ke da nisan kilometa 152 da birnin Bangui, sassan da ke rikici da juna na tafka kazamin fada tsakaninsu.
Duk da cewa babu alkaluma dangane da yawan wadanda suka rigamu gidan gaskiya, amma kuma sojoji da suka ji rauni a Bossambele na tururuwa a babban asibitin Bangui. Wannan ne ma ya sa 'yan kasar fadawa cikin damuwa ba, saboda tashe-tashen hankula sun bazu zuwa wasu sassa na kasar. Tuni ma wasu al'ummar kasar suka fara danganta abin da ke faruwa da rikicin da ya faru a 2012-2013 wanda ya kai ga hambarar da Francois Bozize tare da jefa kasar cikin yakin basasa. Saboda haka ne wasu ke ganin cewa da kamar wuya a gudanar da sahihin zaben 'yan majalisa da na shugaban kasa a ranar Lahadi mai zuwa
Kawunan 'yan takarar a tagwayen zabukan sun rabu biyu: Wasu na fatan ganin a dage zaben har sai komai ya daidaita, yayin da gwamnati ke ci gaba da nacewa kai da fata sai an gudanar da shi a ranar da aka tsara. Su kuwa kasashen Rasha da Ruwanda suna kai wa Shugaba Archange Touadera goyon bayan sojoji domin ya yi nasarar murkushe 'yan tawaye da ke da daurin gindin tsohon shugaban kasa Francois Bozize. Wannan ne ya sa gwamnatin jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ke zarginshi da zama kanwa uwar gami na rikice-rikicen da ake fama da su, inda ta bayyana cewa Bozize ya kudiri aniyar amfani da 'yan tawaye wajen ha,barar da gwamnatin farar hula.
Tagayyara da halin matsi a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya
Bayan juyin mulki a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a bara, rikici a kasar ya ta'azzara. Wannan ya sa mutane yin hijira wanda kuma ba za su iya ba suke fadi-tashi don su rayu. Wasunsu sun fake a filin jirgin saman Bangui
Hoto: Kriesch/Scholz/DW
Neman mafaka a filin jirgin sama
Lamura a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun dagule bayan da aka yi juyin mulki a kasar a bara. Musulmi da kiristoci na yakar juna wanda hakan ya daidaita mutane kimanin miliyan daya. Galibin musulmin da ke babban birnin kasar sun gudu. Wanda suka rage kuma sun nemi mafaka a filin jirgin saman birnin na Bangui.
Hoto: Kriesch/Scholz/DW
Asarar komai na rayuwa
Mijin Jamal Ahmed ya adana 'yan kudade don shi da iyalinsa su yi amfani da shi wajen gudun hijira amma ya yi asarar kudin da ma ransa bayan da 'yan tawayen anti-Balaka suka farwa kauyensu. Tun bayan wannan lokacin Jamal Ahmed na zaune ne a sansanin 'yan gudun hijira da ke filin jirgin sama. Ta ce: ''ban san kowa ba a nan, bani da komai kuma ban san ya zan yi ba"
Hoto: Kriesch/Scholz/DW
Fata na sake ganin jikoki
Fatu Abduleimann 'yar shekaru 84 da haihuwa na daga cikin wanda suka fi tufa a sansanin 'yan gudun hijira. A shekaru 10 da suka wuce ta shiga matsi na rayuwa iri-iri amma kuma bata taba ganin matsala irin wannan ba. Abin kawai da ke kwantar mata da hankali shi ne galibin yaranta na gudun hijira a kasar Cadi. Abu guda ta ke fata yanzu shi ne ta sake ganin jikokinta
Hoto: Kriesch/Scholz/DW
Gari ya zama tamkar makabarta
Baya ga cikin sansanin 'yan gudun hijira, galibin musulmin kasar sun fice daga cikinta. A watannin da suka gabata wata unguwa mai suna ''Kilometer Five'' cibiya ce ta musulmi. Kimanin musumi dubu 100 ne a baya suka zauna tare da yin aiyyukansu a wannan unguwa da ke da nisan kilomita 3 daga tsakiyar Bangui. Yanzu haka musulmi kalilan ne kawai suka rage kazalika an rufe duk shagunan unguwar.
Hoto: Kriesch/Scholz/DW
Jiran lokacin da ya dace
Kusan duk musulmin da ke suka rage a unguwar Kilometer Five na fatan abu daya ne wanda bai wuce barin unguwar ko kasar ba. Motocin da za su kwashe su zuwa kasashe mato wanda suka hada da Cadi ko janhuriyar Kamaru a shirye suke su tashi sai dai sojin da za su bawa jerin gwanon motocin kariya na ta daga ranar tafiya.
Hoto: Kriesch/Scholz/DW
Birni mai sansanonin 'yan gudun hijira
Ba musulmin Bangui ne kadai ke gudun tsira da ransu ba, har ma da sauran jama'a. Kusan ko ina a birnin akwai tantuna inda kiristoci da mabiya addinin gargajiya ke zaune don tsira da rayukansu da fatan samun tallafi saboda gudun kar musulmi su afka musu ko kuma don basu da abincin da za su ci.
Hoto: Kriesch/Scholz/DW
Yunkurin bada tallafi
Pastor David Bendima ya taimakawa kimanin mutane dubu 40 da suka gujewa rikicin kasar wajen samun mafaka a harabar majami'arsa. To sai dai duk da wannan, limamin na addinin Kirista ya ce ba zai iya tabbatar da tsaron mutanen ba kamar yaddda ya ke cewa: ''Kowane dare mu kan ji harbe-harbe da fashewar gurneti, mutane a firgice suke''
Hoto: Kriesch/Scholz/DW
Karancin samun abubuwan masarufi
Chancella Damzousse 'yar shekaru 16 da haihuwa na zaune a wani kauye da ke da tazarar rabin awa daga Bangui. A nan ta na yin abincin dare ne inda ta ke cewa ''wake da ridi ne kawai mu ke da shi''. Wannan dan abin ne kuma za a girkawa mutane 15. Tun bayan da 'yan tawaye musulmi suka lalata kauyen da kashe kiristoci da dama, mutanen gidan su Chancella sun ba makotansu da dama mafaka.
Hoto: Kriesch/Scholz/DW
Masu aikata laifi da kuma wanda laifin ke shafa
Wannan dan kungiyar 'yan tawayen anti-Balaka ne ke tsaye kusa gidansu Chancella. Layu da gurun da ya sa kan kare shi daga duk wani hari kammar yadda ya fada. Aikinsa shi ne ya kare mutanen kauyen daga harin 'yan tawaye da ba sa shiri da su. To sai dai wannan kariya da ya ke badawa na maida hankali ne ga kiristoci kawai. Galibin musulmin kauye sun fice, wasu kuma an kashe su.
Hoto: Kriesch/Scholz/DW
Fata na samun karin karfi
Ya kamata a ce sojin kungiyar tarayyar Afirka da na Faransa su dubu 7 su tabbatar da zaman lafiya a wannan kasa. Wannan ne ya sa kungiyar tarayyar Turai ta ke ta kokarin ganin an kara yawan wannan runduna, sai dai hakarta ba ta cimma ruwa ba. Yanzu haka halin da mutane ke ciki na kara tabarbarewa a kullum.
Hoto: Kriesch/Scholz/DW
Hotuna 101 | 10
Kasashen da ke makwabtaka na nuna damuwa dangane da rikicin da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ke fama da shi, amma ko daya daga cikinsu kowa da bangaren da yake marawa. Sai dai Jean-Jacques Wondo na cibiyar nazarin lamuran tsaro da siyasa a yankin Tsakiyar Afirka, ya ce sarkakiyar da ke tattare da rikicin Afirka ta Tsakiyan kowa na neman tasa ta fisshe shi: "Imma Shugaba Denis Sassou N’guesso ne ko ko Shugaban Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango Félix Tshisekedi ne, a fakaice suna kokarin wakiltar Faransa wajen neman sansanta rikicin, don kalubalantar kasancewar sojojin Rasha a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya."
A yammacin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, wasu kungiyoyin tawaye uku da suka kulla kawance tsakaninsu sun datse muhimmiyar hanya da ake amfani da ita wajen shigar da kayayyakin bukatun yau da kulum a Bangui baban birnin kasar.