Rikici kan iyakar Yuganda da Kongo
August 3, 2012Hukumomin a kasar Yuganda sun bada sanarwar kulle kan iyakar ƙasar da Jamhuriyar Demokraɗiyyar Kongo bayan wani faɗan da ya barke kan iyakokin kasashen biyu tsakanin mayakan ƙungiyar Mai-Mai da dakarun gwamnatin Kongo a yankin Kisandi da ke arewacin kasar. A cewar wani gidan rediyon kongo mai zaman kansa,wasu mutane dauke da makamai daga yankin Ruwenzori ne suka kai hari ga wani ofishin 'yan sandan da kuma ofishin shari'ar garin. To sai dai bayan sa'o'i a na bata-kashi tsakanin ɓangarorin biyu, dakarun gwamnatin sun samu nasarar kwace ofisoshin daga hannun 'yan tawayen.
Wani mai magana da yayun ministan harakokin cikin gidan Yuganda ya ce gwamnatin ta ɗau wannan matakin ne don kaucewa abun da ka iya biyo baya.
Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Mohamad Nasiou Awal