1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaSomaliya

Somaliland: Rikici ya halaka mutane

Lateefa Mustapha Ja'afar
August 25, 2023

Kimanin mutane 20 ne aka tabbatar da cewa sun halaka a yankin Somaliland na Somaliya da ke da kwarya-kwayan 'yancin cin gashin kai, a kasar da ke yankin gabashin Afirka mai fama da rikici.

Somaliya | Somaliland | Tuta | Rikici
Tutar Somaliland mai kwarya-kwaryan 'ynci daga SomaliyaHoto: Valerio Rosati/PantherMedia/IMAGO

Wata sanarwa da ba a kai ga tantance ta ba ta ruwaito dagacin yankin Garad Jama Ismael na tabbatar da afkuwar lamarin, inda ya ce gungun tsageru masu rike da makamai ne suka kai hari a kan sansanonin sojojin yankin na Somaliland da ke garin Laascaanood. Irin wadannan hare-hare a garin na Laascaanood da rikici ya rincabe a farkon wannan shekara da muke ciki, na neman zama ruwan dare. Yankin  Somaliland da Puntland da dukansu ke da kwarya-kwaryan 'yanci daga Somaliya dai, na ikirarin mallakin garin na Laascaanood tare da zargin juna da kai hare-haren.