1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

PDP: Fuskantar adawa ko rikicin cikin gida?

Muhammad Bello LMJ
August 10, 2022

Har yanzu rigimar babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya na ci gaba da tsananta, ko da yake dai gaggan 'yan jam'iyyar na ci gaba da kokarin dinke barakar da ta afku tun bayan zaben fitar da dan takarar shugaban kasa.

Najeriya | PDP | Adawa
Ko rikicin cikin gida zai bar PDP ta yi tasiri a zabukan Najeriya na 2023?Hoto: DW/K. Gänsler

Rigimar kan batun makomar gwamnan jihar Rivers da shi ma ya tsaya takara, kuma ya ke ganin har yanzu ba a yi masa adalci ba da ta shugaban jam'iyyar Iyorchia Ayu da kuma tunkarar zabukan na 2023 da ke tunkarowa a kasar. Tun kafin zaben jam'iyyar na fidda gwanin da zai tsaya takarar shugaban kasa, an tabbatar adawa tsakankanin 'yan takarar ta zafafa musamman tsakanin gwamnan na jahar Rivers Nyesom Wike da gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwa da kuma Alhaji Atiku Abubakar da ya lashe zaben daga bisani. Gwamnan jihar ta Rivers Wike ya koka cewar ba a yi masa adalci ba, kuma daga dukkaninalamu ya zuciya matuka. Yayin da kuma dan takarar na PDP Atiku Abubakar ya zo fidda wanda zai zama mataimakinsa a takarar ta 2023 nan ma aka yi wa gwamnan ba-zata, inda Atikun ya dauki gwamnan jihar Delta Patrick Okowa a maimakon Wike din.

Dakta Ifeanyi Arthur Okowa da Iyorchia Ayu da Atiku AbubakarHoto: PDP/Facebook

Kuma hakan ya dada hassala Wike ta yadda har kawo yanzu gaggan 'yan jam'iyyar na ta kokarin cimma maslaha da shi, domin a tafi tare a fuskanci zabukan na 2023 na kasar. Sai dai ga dukkan alamu Wike din yaki sakkowa daga dokin naki illa ma dai ya ci gaba da mu'amala da gaggan jam'iyyar APC mai mulki, yanayin kuma da ke dada dama lissafin ga PDP. A satin da ya gabata dai, jam'iyyar ta PDP ta kafa kwamitin mutane 14 domin sasanta tsakanin Wike din da ake ganin na da karfi kwarai a jam'iyyar da kuma Alhaji Atiku Abubakar da yanzu ke zaman dan takarar shugaban kasa na PDP. Gwamna Wike dai ya bukaci ayi gaggawar sauke shugaban jami'yyar ta PDP Iyorchia Ayu daga mukaminsa domin nada wani daga kudancin kasar, abin da kuma shi Atikun ya sa kafa ya shure tun farko bisa hujjar cewar hakan ya saba da dokar jam'iyyar.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani