1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici na kara kazanta a jam'iyyar PDP

LateefaJuly 22, 2013

Ya yin da ya rage shekaru biyu a gudanar da babban zabe a Tarayyar Najeriya, jam'iyyar PDP da ta kwashe shekaru 16 ta na mulkar kasar na kara shiga rudani.

Hoto: DW/U.Haussa

A yayin da gwagwarmayar mallakar ruhin jamiyyar PDP dama makomar Tarrayar Najeriya nan da shekara biyu ke kara kamari da daukar fasali, 'yan biyar na gwamnonin dake jagorantar adawa da Shugaba Good- Luck Jonathan sun yada zangonsu cikin jihar Neja da nufin tattauna makomar kasar da manyan 'ya'yanta.

Daga dukkan alamu dai sun kai ga kunar da basu tsoro na hayaki, ga 'yan biyar na gwamnonin jamiyyar PDP wadanda ke jagorantar adawa da Shugaba Jonathan, da kuma suka yada zangonsu na uku cikin tsawon mako guda a tafiyar tabbatar da sake maida dimokaradiyar kasar bisa turbar da suke yiwa kallon dai dai. A karshen makon jiya ne dai gwamnonin suka dira a garin Abeakuta da nufin tozali da tsohon shugaban kasar Chief Olusegun Obasanjo, da ake yiwa kallon dodo ga siyasar kasar da kuma ake zargi da daure gindi cikin rawar da ta kai ga tada hankali na fadar gwamantin kasar ta Aso Rock.

Tsohon shugaban kasa a Tarayyar Najeriya Olusegun ObasanjoHoto: AP

Ko bayan Obasanjon dai gwamnonin da suka hada da Babangida Aliyu na jihar Neja da Rabi'u Musa Kwankwason dake Kano da kuma Murtala Nyako dake zaman gwamna ga jihar Adamawa sannan kuma da Sule Lamido dake ta Jigawa dai, sun kuma kai kansu ya zuwa can Nejar inda suka share tsawon sa'oi suna wata ganawar da tsofaffin shugabannin kasar ta Najeriya biyu Janar Ibrahim Babangida da kuma dan Uwansa Abdussalamu Abubakar dake birnin, ziyarar kuma da a cewar Gwamna Babangida Aliyun ke da ruwa da tsaki da halin da siyasar kasar ta Najeriya ke tafiya kai yanzu haka.

To sai dai kuma ko ta ina kofar gyaran ke a kwai a tunanin gwamnonin PDP dai ana kuma kallon ziyarar a matsayin wani kokari na neman goyon bayan manyan masu fada a jin kasar ta Najeriya a cikin sabon yakin mallakin ruhin jam'iyyar da zakaran gwajin sa ke zaman karamin taro na kasa da PDP ta tsara gudanar dashi a karshen watan gobe na Augusta, goyon bayan kuma da a cewar Dr Umar Ardo dake zaman masani na siyasa kuma dan jam'iiyar PDP a jihar Adamawa, ya zama wajibi ga duk wani mai son tasiri a cikin harkoki na siyasar Tarrayar kasar a nan gaba.

Hoto: DW/U.Haussa

Dole kanwar naki dai ce ta kai ga shi kansa shugaban dake ci yanzu sauka daga dokin girma domin maida kansa da ga Obasanjon da ya ziyarta a garin na Abeakuta, 'yan sa'oi kafin sauraren gwamanonin da majiyoyi suka ce sun shaidawa Obasanjon basu yarda shugaban ya zarce ba. A Talatar ne dai aka tsara gwamnonin zasu nufi Abuja domin tozali da Janar Yakubu Danjuma da shima ke fada a ji cikin siyasar kasar, duk dai a kokari na karkatar da akalar mulki ya zuwa sashen arewacin kasar ta Nijeriya.

To sai dai kuma ya zuwa yanzu, babban rikicin dai na zaman na jam'iyyar da karkatar ta ko ina, ke iya shafar burin ta na sake cin zabe a kasar, wani sabon kawance a tsakanin Arewa maso gabas da 'yar uwarta ta yamma da kuma sashen kudu maso yammacin kasar dai na nufin karkatar kusan kaso 70 cikin dari na daukacin kuri'un kasar a zabukan dake tafe, a bun kuma da 'yan adawar kasar na APC ke fatan rikicin zai musu amfani ya zuwa tabbatar da burin su na kawo karshen ikon jamiyyar na shekaru 16.

Shi kuwa ana nasa bangaren Isa Tafida Mafindi dake zaman daya daga cikin iyaye ga PDP, cewa ya yi jam'iyyar ta su na da karfin shawo kan rikicin tare da tsallake shi domin nasara a nan gaba. A bun jira a gani dai na zaman suddabarun 'ya'yan gidan wadatar da ya zuwa yanzu suka saki rakuminsu babu akala cikin dajin kasar mai tsidau da karangiya ba adadi.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita:Lateefa Mustapha Ja'afar/ U.A