Rikicin kan iyaka, Soma da Kenya
January 25, 2021Talla
Hukumomin Somaliya sun ce sojojin Kenya sun kutsa kai cikin garin Bulohawo a lardin Jubaland domin kai hare-hare a kan dakarun gwamnati, sai dai Kenya ta musunta zargin. Jubaland yanki mai kwarya-kwarya 'yancin gashin kai da ke a kudancin Somaliya kan iyaka da Kenya, ya kasance musababbin rikicin tsakanin makobtan biyu wato Kenya da Somaliya.