1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango

Kwango ta kai karan Apple

Nikolas Fischer LMJ
December 20, 2024

Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ta zargi kamfanin Apple da amfanin da ma'adinan da aka haka a kasarta ta haramtacciyar hanya.

Hoto: picture alliance/Imaginechina/dpa/L. Shengli

Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwangon dai ta zargi kamfanin na Apple da amfani da albarkatun karkashin kasa da aka haka a kasarta ba bisa ka'ida ba, wadanda suka hadar da tin da tantalum da tungsten da kuma zinare. Kungiyoyin da ke rike da makamai a kasar, na daga cikin wadnda suke hakar ma'adinann a Kwango. Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwangon ta dora zarginta ne musamman a kan rukunin kamfanonin Apple din na Faransa da Beljiyam da ta ce suna safarar ma'adinan nata da aka haka ta haramtacciyar hanya aka bi da su ta Ruwanda daga yankunan kasar da suke fama da rikici. Guda daga cikin wadannan yankuna shi ne garin Goma da ke zaman babban birnin yankin arewacin Kivu da ke gabashin Kwango. Kan wannan batu, ga abin da wasu mazauna yankin suka shaidawa DW:

Hoto: Johannes Meier/streetsfilm

"Ina ganin Apple tamkar wani kamfanin ne na 'yan mafiya, kuma ina goyon bayan gwamnati. A ganina tilas suna da shaidar da suka tanada, shi ya sa suka yi wannan zargin. Kamfanin Apple ina ganin aikin mafiya ne, a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango." Ita kuwa wannan cewa take: " Shigar da kara bayan tsawon shekaru, ba lokacin da ya dace ba ne." Ita kuwa a nata ra'ayin wannan cewa ta yi: "Karfin gwiwar shigar da kara, mataki ne da ya kamata a bigire mai kyau domin samar da mafita."

Hoto: Johannes Meier/streetsfilm

Cikin wata sanarwa da kamfanin na Apple ya fitar, ya sanya kafa ya yi fatali da wannan zargi yana mai cewa sun ma bukaci wadanda ke samar musu da ma'adinan su bi duka ka'idojin da aka gindaya wajen hakar ma'adinan. Apple din ya ce sakamakon yadda yaki ya yi kamari, ya sanya ya bukaci masu samar da kayyaykin da su dakatar da ayyukan da suka shafi wadannan ma'adinai na tin da tantalum da tungsten da kuma zinare daga Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da Ruwanda. Sai dai a ta bakin daraktan cibiyar sanya Idanu kan ,ma'adinan karkashin kasa a Afirka wato African Natural Resources Watch Emmanuel Umpula akwai lauje cikin nadi, domin kuwa safarar ma'adinan Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwangon ta haramtacciyar hanya ne dalilin da ya sa yakin ya ci gaba da ta'azzara. Ya kara da cewa: "Kowa ya sani akwai wurare a wadannan kasashe, wadanda ake sarrafa ma'adinan da aka hako ta haramtacciyar hanya daga Jamhuriyar Dimukuradiyya Kwango." Shi ma a nasa bangaren mamba a Hukumar Bayar da Shawarwari kan kungiyoyin farar hula da ke yankin Kudancin Kivu Hypocrate Marume na da ra'ayin cewa: "A wajenmu al'ummar gabashi, wannan wani abu ne na kwantar da hankali.

Hoto: Johannes Meier/streetsfilm

Hakan ce ta sanya muke kira ga sauran kungiyoyi masu zaman kansu, su marawa lauyoyinmu baya. Ta haka ne za mu samu damar yin ido biyu da matakan da ake dauka kan wannan matsala da suka haifar, ta hanyar tattaunawa da 'yan tawaye."Majalisar Dinkin Duniya da kwararru da kuma masu rajin kare hakkin dan Adam, sun nunar cewa ana zargin wadannan kungiyoyi masu rike da makamai a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango masu tayar da kayar baya a yankunan da ke fama da rikici a kasar da kashe fararen hula da aikata fyade da sata da sauran muggan laifuka.