1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici tsakanin Siriya da Turkiyya ya fara shafar Rasha

October 11, 2012

Turkiyya ta saki wani jirgin fasinjar Rasha zuwa Siriya bayan tantance ko yana ɗauke da makamai ne ko kuma a'a.

epa03428024 A Syrian passenger plane is seen after it was forced to land at Ankara airport, Turkey, 10 October 2012. The plane was headed to Damascus from Moscow with 35 passengers on board, according to Turkish media. The Turkish air force sent several F-16 fighter jets to force the Airbus plane on suspicion it was carrying weapons on board. Russia is the most important source for weapons for the regime of President Bashar al-Assad. A large section of the Syrian opposition is based in Turkey. EPA/CEM OKSUZ/ANADOLU AGENCY EDITORIAL USE ONLY/NO SALES/NO ARCHIVES (recropped version +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: picture-alliance/dpa

Hukumomi a ƙasar Turkiyya sun saki jirgin fasinjar Rasha da ke kan hanyarsa ta zuwa Siriya bayan da mahukunta a birnin Ankara fadar gwamnatin Turkiyya suka yi anfani da wasu jiragen yaƙi biyu domin tilastawa jirgin sauka a birnin bisa zargin yana ɗauke da makamai zuwa Siriya. Ministan kula da harkokin wajen Turkiyya Ahmet Davutoglu yace akwai wasu kayayyakin da jami'an Turkiyya suka ƙwace daga cikin waɗanda jirgin ke ɗauke da su, amma ba tare da ya bayyana nau'in kayayyakin ba.

Rasha dai ita ce babbar ƙasar da ke samarwa Siriya makamai, kuma sau ukku tana hawan kujerar naƙi dangane da ƙudirin sanyawa gwamnatin shugaba Assad takunkumi a kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya. Tilastawa jirgin na Rasha ya sauka shi ne jerin taƙaddama na baya bayannan da ke yaɗuwa a tsakanin ƙasashen duniya sakamakon rikicin ƙasar Siriya.

A cikin tsukin mako guda kuma Turkiyya da Siriya sun yi ta musayar harbe-harben makaman roka ta kan iyakokin su, inda babban hafsan sojin Turkiyya yayi gagaɗin cewar Turkiyya za ta mayar da martani mai tsanani muddin dai aka ci gaba da jefa makamai a cikin yankunan ta.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu