1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mali: Rikici tsakanin 'yan tawaye da gwamnati

December 23, 2022

Gamayyar kungiyoyin 'yan tawaye na Mali ta sanar da janyewa daga yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a shekarar 2015 tsakaninta da gwamnatin kasar.

Taron sanya hannu a yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin 'yan tawaye da gwamnatin Mali a shekarar 2015Hoto: Habibou Kouyate/AFP/Getty Images

Shugabannin Kungiyoyin da ke gwagwarmaya da makamai a Mali sun yi ikrarin cewa gwamnatin Bamako na yi wa yarjejeniyar zaman lafiya rikon sakainar kashi. Gamayayyar kungiyoyin ta zargi majalisar mulkin sojin kasa da rashin mutunta yarjejeniyar da kuma yin biris da batun tabarbarewar tsaro a wasu yankunan kasar.

A cikin sanarwar hadin gwiwa da gamayyar ta fitar, ta ce matakin janyewar zai fara aiki daga yanzu har zuwa lokacin da za su gana da masu shiga tsakani na kasa da kasa.

A shekarar 2015 ce dai bangarorin suka sanya hannu a yarjejeniyar zaman lafiya a kasar Aljeriya, wanda ya kawo karshen fada tsakanin dakarun Mali da kuma 'yan tawaye ciki har da ta Abzinawa ta CMA da ke neman dara kasar gida biyu. Sai dai kasar ta ci gaba da fuskantar hare-hare daga kungiyoyin da ke ikrarin jihadi.