1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici ya ɓarke a Siriya bayan tsagaita buɗe wuta

April 13, 2012

Masu bore a Siriya sun yi fito-na-fito da jami'an tsaro akan Iyakar Siriya da Turkiyya.

Source News Feed: EMEA Picture Service, Germany Picture Service Demosntrators carry mock coffins and shout slogans during a protest against Syrian President Bashar al-Assad in Izmir April 7, 2012. Syrian troops pounded opposition areas on Saturday, activists said, killing 43 people in an offensive that has sent thousands of refugees surging into Turkey before next week's U.N.-backed ceasefire aimed at staunching a year of bloodshed. REUTERS/Stringer (TURKEY - Tags: POLITICS CIVIL UNREST)
Boren adawa da shugaba Assad na Siriya a TurkiyyaHoto: Reuters

Rahotanni daga ƙasar Siriya na cewar an samu wata taho mu gama tsakanin masu zanga-zanga da dakarun gwamnati a yankunan da ke kan iyakar ƙasar ta Syria da Turkiyya.

Rikicin dai ya ɓarke ne sanadiyyar harbin da dakarun gwamnati su ka yi na kan mai uwa da wabi yayin da wasu mutane su ka gudanar da zanga-zanga a dandalin Assi, wanda hakan ya yi sanadiyyar rasuwar mutum guda.

Baya ga haka an kashe mutum guda daga cikin masu zanga-zanga a ƙauyen Nawa dake kudancin Deraa, da ma dai ƙarin mutum guda a arewa maso yammacin gundumar Idlib, lamarin da ya sanya dubun-dubatar 'yan ƙasar gudanar da zanga-zanga a wurare da dama.

Wannan dai na zuwa ne kwana guda bayan fara aiki da shirin wanzar da zaman lafiya da manzon musamman na Majalisar Ɗinkin Duniya Kofi Anan ke jagoranta.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Mohammad Nasir Awal