1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fada ya tilasta wa daruruwa barin gidajensu a Kamaru

Abdul-raheem Hassan RGB
December 31, 2021

Mutane akalla 100,000 sun tsere daga gidajensu a sakamakon wani sabon rikicin makiyaya da masunta da kuma manoma a kan iyakar Kamaru da Chadi.

Sudan Symbolbild Wirtschaftskrise
Hoto: Simon Wohlfahrt/AFP

Sabon rikicin makiyaya da masunta da kuma manoma a kan iyakar Kamaru da Chadi, ya tilasta wa akalla mutane 100,000 barin gidajensu, kuma yanzu haka, Hukumar Kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNHCR, ta ce dubban 'yan gudun hijirar Kamaru na cikin wani hali a sansanonin 'yan gudun hijira a kasar Chadi. 

A farkon watan Disamban 2021, takaddama ta kaure tsakanin makiyaya da manoma da masunta kan ragowar albarkatun ruwa, hukumomin kula da yanayi, sun ce barazanar sauyin yanayi na daga cikin abin da ke kara haddasa rikicia tsakanin al'umma da ke rige-rigen samun albarkatun kasa, musanman ruwa don bayin amfanin gona da shayar da dabbobi da masu kamun kifi a yankin arewa mai nisa a Kamaru, inda sama da mutum dubu tamanin da biyar, suka tsere zuwa kasar Chadi, kusan dubu goma sha biyar, an tilasta musu neman matsuguni a cikin gida.

Daruruwa na tsugune a sansanin 'yan gudun hijiraHoto: Panagiotis Balaskas/ANE/Eurokinissi/picture alliance

Yawancin sabbin mutanen da ke gudun hijira zuwa kasar Chadi yara ne kanana, sannan kashi 98 cikin 100 na matasa da ke tsere wa rikicin mata ne. Hukumar da ke kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce, a halin da ake ciki 'yan gudun hijirar na cikin wani yanayi na bukatar agajin gaggawa. 

Adadin wadanda suka mutu a rikicin ya zuwa yanzu, ya karu zuwa mutane arba'in da hudu a yayin da sama da dari suka jikkata, a baya-bayan nan, an samu mutuwar mutane ashirin da biyu da jikkatar wasu talatin, an kuma kona kauyuka kusan dari da goma sha biyu.

Yan gudun hijira na fuskantar karancin abinciHoto: Jack Taylor/Getty Images

Yanzu haka, a yayin da 'yan gudun hijira ke jibge a Chadi a sakamakon sabon rikicin daga kan iyakar Kamaru da Chadin, masana na cewa, ruwan saman tafkin Chadi ya ragu da kashi 95 cikin dari a cikin shekaru 60 da suka gabata, matakin da ke tsananta halin rayuwa ga mazauna kusa da tafkin kasar ke fuskanta. UNHCR ta yi kiran gaggawa ga kasashen duniya da su ba da goyon baya don taimakawa 'yan Kamaru da rikicin ya tilastawa gudun hijira.