An kama mutum sama da 300 daga Masallacin Kudus
April 5, 2023Rikici ya barke a tsakanin Isra'ila da Falasdinu, in da rahotanni ke cewa, 'yan sandan Isra'ila ne suka kai hari kan dandazon masu ibada a masallacin Al-Aqsa da ke a birnin Kudus, 'yan sandan sun kuma yi kame na mutanen da ke ibada a cikin Masallacin, lamarin da ya kai ga barkewar artabu tsakaninsu da musulmai Falasdinawa. Yan sandan na Isra'ila na cewa, martani ne kan wasu rokoki akalla tara da aka harba mata a daren ranar Talatar da ta gabata.
Kungiyar agaji ta Red Crescent ta Falasdinu ta ce, kawo yanzu, Falasdinawa bakwai suka samu raunuka daga harsasan roba da aka harba kansu a lokacin arangama da 'yan sandan Isra'ila a cikin masallacin na Al-Aqsa. Mutum sama da dari uku aka kama daga Masallacin tun bayan barkewar rikicin na daren Talatar da ta gabata ya zuwa wayewar garin wannan Laraba.